Mun Yi Garkuwa Da Mahaifina Saboda Ba Ya Kyautata Mana , Inji Ibrahim Babatunde
Mun Yi Garkuwa Da Mahaifina Saboda Ba Ya Kyautata Mana , Inji Ibrahim Babatunde
Daga Haji Shehu
Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun damke wani matashi dan shekaru 20 da laifin hadin baki da wasu abokan sa uku masu shekaru 19, inda sukayi garkuwa da mahaifinshi.
Matasan sun tsare tsohon har na tsawon kwanaki uku tare da karbar diyar naira miliyan daya a hannun iyalansa.
Matashin mai suna Ibrahim Babatunde ya tabbatarwa jami’an tsaro cewar mahaifinsa yana da dukiya amma baya kyautata musu, kullum sai yawan yin aure barkatai, wannan matsin shi ya sanyashi aikata wannan aika-aikan.
Ibrahim ya kara da cewar babu wata hanya da zai bi ya sami kudi daga aljihun maifin shi face wannan hanya ta yin garkuwa dashi.
Izuwa yanzu dai an garzaya da Ibrahim zuwa wani wajen da baa bayyana sunashi ba domin cigaba da tatsar bayanan sirri, ganin cewar ana zargin wasu masu shekarun daya dara nashi cikin wannan aika-aika.
Rahoto. Facebook/Rariya