Me ye Gaskiyar Cewa Barr Solomom Dalung Ya Karbi Musulunci?
ME YE GASKIYAR CEWA BARR. SOLOMON DALUNG YA KARBI MUSULUNCI?
Daga Affan Buba Abuya
Barrister Solomon Dalung, Ministan Matasa Da Wasanni, yakai ziyara wajen Tafsir na Sheikh Dr Isa Ali Pantami da ya gabatarwa a Masallacin Anur-Mosque, Wuse II, Abuja a Ranar Alhamis.
Sheikh Pantami yayi masa maraba da zuwa tare da nasiha irin ta Malamai da kira ga Barr Solomon Dalung da yayi Imani da Annabi Muhammad S.A.W, ya shiga Addinin Musulunci.
A jawabin sa Barr. Dalung yace ya samu goron gayyata da Malam Pantami yayi masa kuma zai yi Tunani Akai.
Domin haka Barrister Solomon Dalung bai karbi Musulunci ba a wajen Tafsir na Malam, Amma muna masa Addu’a Allah yasa ya amshi wannan goron gayyata da malam yayi masa na shiga Musulunci da shi da sauran wadanda ba musulmai ba. Amin.