Kannywood

Mawaki Ado Gwanja Ya Sha Duka A Hannun Jami’an ‘Yan Sanda Na Kano

Mawaki Ado Gwanja Ya Sha Duka A Hannun Jami’an ‘Yan Sanda Na Kano  

Daga Habu Dan Sarki

Fitaccen mai wasan barkwancin nan kuma mawakin Hausa wanda aka fi sani da Ado Gwanja ya sha kashi a hannun wasu fusatattun jami’an ‘yan sanda dake aiki tare da caji ofis na ‘Yan Akwa dake cikin birnin Kano, inda ya je domin belin wani yaron sa da aka kama.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne sanadiyyar hayaniyar da ta kaure tsakanin Gwanja da ‘yan sandan bayan da suka nemi ya biya naira dubu 10 domin belin yaron nasa, inda  shi kuma mawakin ya kafe kan ba zai bayar ba, domin kuwa ya san beli kyauta ne.

Jin hayaniyar dake faruwa tsakanin maigidansa da ‘yan sandan dake tsare da shi, a cewar wani jami’i da al’amarin ya faru kan idanunsa, sai yaron Gwanjan da ake tsare da shi bisa laifin yawon dare, mai suna Chassis ya sa baki don a hayaniyar da ake yi don kare mutuncin maigidan sa, abin da ya haifar masa da hucewar fushin ‘yan sanda a kansa.

Shi ma Gwanja da ya ga dukan ya wuce misali sai ya shiga tsakani domin ya kwaci yaronsa, ai kuwa sai suka hada da shi suka lakada musu dukan kawo wuka.

Yanzu haka dai lamarin na gaban kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, yayin da ake tsare da dan sandan da ya haifar da wannan danyen aiki a hedkwatar ‘yan sanda dake Shahuci.

©Zuma Times Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA