Kannywood

kannywood:An kaddamar da kannywood box office



Sun bayyana haka a wani taron ganawa da manema labarai da sauran kungiyoyi dake karkashin Kannywood

Masana’antar Kannywood ta kasance masana’anta wadda ta fi kowacce a arewacin Nigeria samar da ayyukan yi ga matasa cikin kankanen lokaci, amma kasuwanci a cikinta ya gurgunce tsawon shekaru sakamakon dogaro da hanya daya ta samar da kudaden shiga (wato kasuwannin siyar da CD/DVD). A lokatai da dama mutane da dama sun yi yunkurin kawo canji a tsarin kasuwanci amma abin ya ci tura.

Da alama cewa a wannan karo haka zai cimma ruwa. Dalili kuwa shine kamfanin shirya fina-finai na MOTION PICTURE PRODUCTIONS LTD tare da hadin gwiwar CERTIS NIGERIA LTD sun zaburo da sabon tunani wanda zai tafi tare da zamani wajen ganin cewa an farfado da harkar kasuwancin fina-finai yadda kowa zai ci moriyar abin, kama daga Gidajen Kallo, Masu shirya fina-finai, kungiyoyin yan fim har ma da gwamnati.
Kannywood Box Office , zai kasance sabon dandamali a daidai lokacin da harkar tattalin arziki ta tabarbare kuma satar fasaha ta kai tsaiko yadda masu saka jari cikin harkar ke guduwa kuma fasaha ke dakushewa. Hanya daya tilo da za’a fito daga cikin wannan duhu shine ta hanyar farfado da Sinimomi. Kiyasi na baya bayan nan na nuna cewa a Jihar Kano kawai, akwai kimanin kananan sinimomi 8,000, wadanda ta hanyar amfani da tsari da fasahar zamani za’a iya cin cikakkiyar moriyar su, wadda zata kawo dinbin arziki ga masana’anatar.

Wannan tunani ya sa shugabannin wadancan kamfuna guda biyu suka yunkura wajen farawa da samar da wata na’ura, wadda su ka kira da YODA. Ita wannan na’ura ta majigi (projector) an tsara ta yadda sai da kati mai ajiyar fasaha kawai za ta iya amfani da ita (memory card) kuma ba wani mai irinta a fadin duniya sai kamfanin CERTIS. Ta wannan hanya za’a tsare duk wani fim da aka saki daga barayin fasaha, domin ko ka sami wannan kati ka saka a wata komfuta ba zai yi amfani ba sai a na’urar YODA.
Dandamanlin zai kasance waliyyin daura aure tsakanin gidajen kallo da masu shirya fina-finai ta hanyar hada yarjejeniya yadda kamfunan za su karbi fina-finai daga hannun masu shiryawa su rika nunawa a gidajen kallo ta hanyar wannan na’ura ta YODA.

An sami gidajen kallo kimanin 200 da za’a fara gwaji da su a karshen watan June, 2017 kuma a kididdigar da su ka yi ya nuna cewa a kalla a rana guda kowanne gidan kallo zai iya samun 7000, wato kaso 47% cikin dari na kudaden da za’a samu, yayin da masu fim za su iya samun 4000 wato kaso 27% a gidan kallo guda inda masu shirya tsarin da kula da shi za su sami 2000 wato kaso 14%, sai hukumar fina-finai wadda za’a rika cire wa harajin 1400 wato kaso 9.8% (maimakon kusan kaso 10-38% da gwamnati za ta iya karba kai tsaye).
Dandamalin ya fitar da tsarin bawa fina-finai aji kama daga A, B da C, wanda kudin da mai shiryawa zai samu ya danganta da ajin fim dinsa, hikimar itace samar da inganci wajen irin fina-finai da za’a rika fitarwa. A shekara guda, wanda yayi fim mai inganci zai iya tashi da kimanin miliyan 42,000,000.

Hakika wannan tsari zai zama wani juyin-juya-hali a wannan masana’anta domin a halin da ake ciki babu wani fim da zai iya wuce sati biyu a kasuwa kuma ribar da za’a samu ba ta taka-kara-ta karya ba.

Wannan sabon tsari zai samar da hanyar kudin shiga kai tsaye ga masu gidajen kallo, da masu shirya fim har ma da gwamnati, ya kuma samar da sabuwar hanya da ake kishirwarta a wannan lokaci da kasuwar fim ta kusa rugujewa.

Sannan gagara-badau shine yakar masu satar fasaha wadanda a yanzu ke lashe kusan kashi 90% na gumin masu shirya fim, domin wannan na’ura ita kadai ce tilo kuma ta sami sahalewar British Council da Alu ja cikin jami’o’in fasaha a duniya wato Massachusetts Institute of Technology (MIT). Sannan za’a bawa kungiyoyi damar samun bayanai da kuma cudanya da sauran masu ruwa da tsaki yadda za’a iya samun cikakken tsari da kowa zai amfana daga gare shi.
A yau, masana’anatar Kannywood ta dogara da siyar da DVD, wanda idan tsarin da aka zo da shi yayi tasiri DVD zai kasance a mataki na 4 bayan matakan Sinimomi da gidajen kallo, gidajen talabijin da na’urar sadarwa (Online irinsu Netflix, IrokoTV da sauransu) sannan ne za’a fara maganar DVD, wanda a kaida lokacin da fim ya kai ga DVD, kamata ya yi a ce mai shirya fim din ya gama mayar da kudinsa har ya fara samun riba, yadda DVD zai kasance ribar kafa.

A karshe muna ganin cewa farawa da tsarin sinimomi da gidan kallo zai kasance dan ba na ganin cewa duk wadannan tsaruka sun zama zahiri yadda wannan masana’anta da ke da dimbin arzikin da ba’a tatsa ta farfado daga cikin mawuyacin halin dakushewar kasuwancinta zuwa ga matakin arziki da fadada izuwa ga sauran jihohin Nigeria da Afurka har ma da duniya.
Hotuna daga ganawan


©pulse.ng

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button