Kannywood

KANNYWOOD: Dawowar Rahama Sadau Harkar Fim Ya Fara Tayar Da Kura


Kamar Yadda kuka sani cewa an dawo da jaruma rahama sadau harkar fim a satin daya gabata wanda kamar yadda alamu yanuna jarumar tadawo da kafar dama domin kuwa sabon fim dinta mai suna rariya yana daya daga cikin jerin fina finan daza’a saki acikin bikin sallah.

Hakan ne yakawo tashin kura a wani bangaren daban musamman ma ga yan uwanta mata abokan harkar tata domin kuwa mafi yawancinsu ba’a son ransu aka dawo da Rahma Sadau ba. sabida suna zaton zata iya hana su rawar gaban hantsi awajen wasu daraktocin kamar Ali Nuhu da Aminu Saira dadai sauransu.

Jaruma Guda Dayace wacce tafito fili ta nuna murna da farin cikin dawowarta harkar wato Aisha Aliyu Tsamiya.
Shin Ko Mene Ra’ayinku Gameda Dawowar jarumar???

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button