Dokoki 9 Masu Tsauri Da Aka Kafa Domin Mashaya Taba Sigari A Kasa Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta kafa wasu dokoki masu tsauri domin mashaya taba sigari a kasa Najeriya.
Ministan Kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya sanar da hakan a taron wayar da kan mutane kan illolin da ke tattare da zukar da taba sigari wanda ake yi a kowace shekara mai taken‘Tobacco: A Threat to Development.’
Taken na wannan shekarar ya na da alaka ne da yadda idan aka samu nasarar dakatar da yawaita shan taba sigari za a sami ci gaban da kasa ke bukata da rage yawan talauci a ake fama da shi.
Ga Dokokin;
1. An hana siyar da sigar wa duk wanda bai kai shekara 18 da haihuwa ba.
2. An hana siyar da sigari kara-kara sai dai kwali.
3. Za a siyar da sigari wanda baya fitar da hayaki da ya wuce gram 30.
4. An hana talla ko kuma siyar da sigar ta kafofin yanar gizo.
5. An hana kamfanonin sarrafa sigari saka baki akan abubuwan da ya shafi kiwon lafiya.
6. An hana amfani da sigari a duk wuraren da yara ko kuma ake kula da yara da kuma duk inda mutane suke wanda ya hada da tashar mototoci, wuraren shakatawa,wuraren cin abinci da makamantansu.
7. Za a hukunta duk duk wani mamallakin wuraren da aka Ambato da ya bari aka sha sigari a wurin sana’ar sa.
8.An hana yin tallata sigari ta kowace kafa ko hanya ko kuma tallafa wa kamfanoni irin haka.
9. A tabbatar an Kiyaye wannan dokoki.