Uncategorized

Bajintarsa A Gasar Kur’ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi Daga Abu Abdur

Bajintarsa A Gasar Kur’ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi

Daga Abu Abdurrahman

Limamin Harami Shaykh Sudais ya sumbaci goshin yaron nan (Amer Falatah) ya kuma fada masa cewa insha Allah shine zai zama limamin Harami nan gaba.

Wannan yaro dan Albarka wanda ya zama abin Alfahari ga mahaifansa, Musulinci da musulmin duniya ya taka rawar gani a musabukar Alqur’ani ta Duniya.

Ameer Falatah dan kasar Malawi shine ya zo na daya a gasar karatun Kur’ani na duniya da aka gudanar.

Da wannane muke kara kira ga iyaye lallai a rage fifita karatun boko na yara sama da karatun Addini 

Domin halin da muke ciki yanzu akwai bukatar kowa ya yi tunani gina al’umma ta gari, mu fara daga gidajen mu, 

✔Kayi tunani da kanka wai shin a family dinku kuna da background na ilimin addini ? 

✔Idan babu ka fara tsarawa daga ‘yay’anka, don kuma ku shiga cikin mafificiyar al’umma. Shima ilimin zamanin yana da amfanu, amma kar a nunawa yara tun suna kanana cewa ilimin bokon yafi daraja. 

Domin Allah (SWT) yayi yabo na musamman ga bayinsa masu haddace Alqur’ani a cikin littafinsa yake cewa:

*”بل هو ايات بينا ت في صدرالذين اوتواالعلم”* 

Ku saurari karatun yaronnan….subunallah

©Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button