Abin Al’ajabi:Wata ‘yar Nigeria ta yanki al’aurar wanda ya yi mata fyade
An gurfanar da wani mutum mai shekara 30 a gabata kotu, bayan yarinyar da ya yi wa fyade ta yanki al’aurarsa, a jihar Katsina da ke arewa-maso-yammacin Najeriya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Gambo Isa, ya shai da wa BBC cewa, asirin mutumin ya tonu ne bayan da ya je neman shaida a wajen ‘yan sanda domin likitoci su duba raunin da yarinyar ta yi masa a al’aura.
Jami’in ‘yan sanda ya kara da cewa an fahimci abin da ya faru ne bayan ‘yan sanda sun yi masa tambayoyi, inda daga nan ne aka gane cewar ya ji ciwon ne a lokacin da yake yi wa wata yarinya fyade da karfin tuwo.
A halin yanzu dai mutumin da ake zargin na gidan wakafi, bayan alkalin kotun majistire, sai Mai Shari’a Fadile Dikko ya dage sauraren karar zuwa 20 ga watan Yulin mai kamawa.
Alkalin ya ce zai mayar da shari’ar ga rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da kuma daraktan gabatar da kara na jihar domin gurfanar da mutumin a gaban babbar kotu, saboda kotunsa bata da hurumin sauraron batun fyade.
Bayanai daga jihar ta katsina na cewa lamarin ya faru ne a wani kango a karamar hukumar Kankara.
Lamarin dai ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayun da ya wuce, amma ya fito fili ne a lokacin da shi mai fyaden ya je asibiti neman magani.
A karkashin doka a Najeriya dole ne mutum ya gabatar da bayanin amincewar ‘yan sanda ga likitoci kafin su duba shi, idan rauninsa ya shafi wasu nau’uka ciki har da harbin bindiga.
©bbchausa_com
Yayi kyau