Uncategorized

Yawancin mata ma’aikata zawarawa ne – Sheikh Daurawa

Yawancin mata ma’aikata zawarawa ne – Sheikh Daurawa

Lakcarori mata suna da aure – Binta Sulaiman
Babu gaskiya a wannan magana – Shugabar Lauyoyi Mata
A wata tattaunawa da Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi da jaridar Daily Trust ya kawo jerin kashe-kashe na mata takwas da suke zawarawa ne a jihar. Sheikh Daurawa ya ce yawancin mata ’yan siyasa da lauyoyi da likitoci da malaman jami’a da ’yan kasuwa da shugabannin makarantun sakandare da manyan sakatarori da ma’aikatan gwamnati zawarawa ne.

Aminiya ta nemi karin bayani daga Sheikh Daurawa inda ya ce wannan magana da ya fada haka take kuma bincike ne ya tabbtar da hakan, “Duk da cewa ba a wani littafi aka rubuta hakan ba, amma kuma ba da ka muka fadi hakan ba. Mu da muke cikin al’umma din muke ganin irin abin da ke faruwa yau da gobe ya sa muka san hakan. Haka kuma mu ake gayyata laccoci da kuma irin wayar da matan ke yi mana cewa mu samo musu mazan aure ko su nemi mu yi musu addu’a, ke nan dole za mu san cewa akwai su da yawa a cikin al’umma,” inji shi.

Game da kowane dalili ne ke kawo yawaitar irin wadannan mata da ba su da aure, malamin ya danganta haka da rashin son aikin mata da maza ke yi. “Daga abin da na fahimta ina ganin babban dalilin hakan shi ne yawancin maza ba su son su ga matansu suna aiki. Wannan kuwa ba wai kawai ya shafi mazan da ba su da ilimi ba ne, har masu ilimi, masu manyan mukamai a gwamnati sun fi son su ga matansu suna zaune a gida,” inji shi.
Sheikh Daurawa ya alaknta hakan da wasu dalilai guda uku da suka hada da tsawon awannin da matan ke shafewa a wajen gidansu ba tare da kula da mazansu da ’ya’yansu ba, baya ga zarge-zargen da ake yi wa matan. “Yawanci mata ma’aikata suna karar da awanni takwas na rana a wajen aiki, ba kowane namiji ba ne zai yarda matarsa ta fita waje ta shafe tsawon awa takwas ba tare da ta tsaya ta kula da abin da ya shafi gidanta da tarbiyyar ’ya’yanta da kuma kula da shi kansa maigida ba. Sannan wadansu matan ba su da kamewa idan sun fita wurin aiki, wanda kuma mazan suna kishin hakan. Akwai misalin wata likita da aikinta ya jawo mutuwar aurenta, na farko mijin yana zarginta da rashin zama a gida a koyaushe har cikin dare a kan kira ta yin aiki, kuma yana zarginta da cewar tana da wani namijin da suke haduwa wanda ya dauke mata hankali a wurin aiki. Haka kuma yana ganin sakamakon kudin da take samu ta kangare masa. Wadanann dalilan suka sa ma’auratan suka yi ta samun matsala har a karshe auren ya lalace,”

 inji Daurawa.
Sheika Daurawa ya kara da cewa:

 “Haka wadansu matan saboda kudin da suke samu, sukan kangare wa mazajensu ma’ana ba su yi musu biyayyar aure yadda ya kamata. Wannan yana daga cikin dalilin da yake sanyawa maza ba su fiye auren mata masu aiki ba.

 Wadansu matan kuma suna ganin sun wuce matsayin wadansu mazan ta fuskar kudi da mukami, wani dalilin kuma shi ne da yawa daga cikin wadannan mata ba su son kishiya, duk da cewa suna fita aiki suna cinye wa mazansu lokacinsu a waje, amma ba su son mijin ya kara aure. Haka kuma ana samun matsala a gidan da aka samu mata biyu daya tana aiki daya kuma ba ta yi. Yawanci irin wadancan mata sukan yi tsalle su ce su ba su yarda ba dole sai an sama musu aiki ko a yanka musu albashi. Wannan yana daga cikin dalilin da yake sanyawa mata ma’aikata ba su samun yin aure.”

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa: “Mafita daga wannan hali shi ne a rika yin aure a kan lokaci, ba mu ce kada a yi karatu ba, amma muna bayar da shawara cewa idan yarinya ta samu miji kada a ce sai ta gama karatu, maimakon haka a yi mata aure idan ya so a yi yarjejeniya cewa zai barta ta ci gaba da karatunta. A hada auren da karatun. Akwai matar da take gaya min cewa da ta san cewa za ta dauki tsawon lokaci ba tare da ta yi aure ba, to da ba ta yi karatu har ta yi aiki ba. Ta gaya min cewa irin mijin da take so ba za ta same shi ba a yanzu. Sannan su kuma mata masu aiki muna kira su rika kame kansu. Su daina mu’amalar da ba ta dace da maza ba ko don gudun zargi. Haka kuma su sani fitar da suke yi wurin aiki na tsawon shekara 35 sun karar da su a waje.

 Sun bar gidansu da yaransu a hannun masu aiki. Ki duba ki gani ke an dauke ki aiki bisa kwarewa ita kuma wacce kika dauka take miki naki aikin a gida ba ki dauke ta bisa wata kwarewa ba.

 Ba ta san ta koya masa cin abinci da hannun dama ba, ba ta san ta koya masa gaskiya da amana da sauran kyawawan dabi’u ba. Ita dai kawai idan yaro ya yi kuka ta ba shi abinci ta kai shi ban-daki. Idan ya ji barci ta kwantar da shi.
 Sai a wayi gari an kare rayuwa a wurin aiki, ’ya’yanki kuma ba su samu tarbiyyar da ta kamata su samu ba. Kun tafi aikin wadansu to ku kuma wa zai yi miki naki aikin a gida? Wadannan matsaloli ne suke haduwa idan mijin ya ga ba zai iya ba a karshe ya rabu da matar, kin ga abin da muke fadi ya tabbata.”

Har ila yau Sheikh Daurawa ya yi kira ga gwamantai da ta yi wata doka da za ta tabbatar da hukunci a kan duk shugabanni ko lakcarorin da aka samu suna yi wa mata barazana. “Akwai mata ma’aikata da dalibai da ke samun kansu a tsaka-mai-wuya, inda ake yi musu barazana cewa ba za a kara musu girma ko ba za su ci jarrabawa ba har sai sun bayar da hadin kai.

 Muna neman a samar da wata doka da za ta samar da wani hukunci a kan irin wadannan mutane, saboda laifin ya yi kama da fyade. Don haka idan an samu irin wadannan mutane a zartar musu da hukuncin fyade kawai. Haka kuma su ma matan a nasu bangaren ita ma idan an ga suna yin kwarkwasa a hukunta su.

 Wannan ne zai sa mu saki jikinmu mu rika barin matanmu suna aiki ba tare da tunanin faruwar wani abu ba. Sannan matan su yi kokari wajen ganin sun sauke nauyin da Allah Ya dora musu na gida ba tare da matsala ba,” inji shi.

Malama Binta Sulaiman lakcara ce a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Bayero (BUK), ta ce “Mu gaskiya matan da ke koyarwa a BUK muna da aure, wadanda ma ake samu ba su da auren za ka tarar mazansu ne suka mutu wadanda kuma harkar kula da ’ya’yansu ya sanya ba su sake yin wani auren ba. Ya kamata malamai su san cewa maganganunsu suna da tasiri a wurin al’umma don haka wannan zai iya kawo ci baya ga harkar ilimin mata a Kano, domin wadansu da suka ji wannan magana har sun fara tunanin hana ’ya’yansu yin karatu mai zurfi. Idan mun duba dama can a baya muke a kasar nan, mu da muke ta son mu samu karuwar mata masu ilimi sai kuma mu ci baya? A kullum mutanenmu suna kin yarda likitoci maza su taba musu mata, to idan har ’ya’yanmu mata ba su yi karatu ba, to yaya za mu yi da waccan matsalar. Yawanci inda ake samun matasala shi ne idan ba a yi dace mata ta samu mijin kirki ba, sai ya rika gasa
da ita, yana ganin yaya za a yi ta kai wani matsayi da shi bai kai ba. To dama akwai wannan tsoro a cikin al’umma, ballanatana kuma yanzu da ake sake rura wutar abin. Wanda ya ga ’yar boko yanzu sai ya ce shi ba zai iya ba. Ni ina tunanin Malam ya yi wannan magana ne cikin jin haushin dokar iyali kawai. Bai kamata ana jin irin wadannan maganganu daga malamai irin su Sheikh Daurawa ba.”
Barista Usaina Aliyu Ibrahim, Shugabar kungiyar Lauyoyi Mata ta kasa, reshen Jihar Kano, ta musanta batun da Sheikh Daurawa ya yi inda ta ce a iya saninta ba ta san lauyoyi zawarawa ba ko wadanda suka dade ba su yi aure ba a cikinsu.

“Dukanmu lauyoyin da ke cikin kungiyarmu muna da aure da ’ya’yanmu da jikokinmu. Idan kika dauke ni yau shekarata talatin da aure. Lauya daya ce na san bazawara a cikinmu, ita ma hakan ya faru ne sakamakon rasuwar mijinta a bara.
A yanzu haka ma duk ta aurar da ’ya’yanta, ’yar autarta za a yi wa aure kwanan nan. Su kuma wadanda ba su taba yin aure ba, yara ne masu kananan shekaru.
Don haka babu gaskiya a wannan magana ko kadan”.

Daga:Aminiyahausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button