Uncategorized

Yadda BudadiyarJami’ar (NOUN) Ta Zama Zakaran Gwajin Dafi A Nijeriya – In ji Obasanjo

Yadda BudadiyarJami’ar (NOUN) Ta Zama Zakaran Gwajin Dafi A Nijeriya – In ji Obasanjo

Daga Isma’il Karatu Abdullahi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa jami’ar karatun budandiyar jami’a ta NOUN na daya daga cikin manyan nasarori da ya samu a lokacin da ya ke shugaban kasa.

Tsohon shugaban kasar, ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron bude cibiyar bincike da nazarin shugabanci na gari ta Olusegun Obasanjo Good Governance and Research Center a dakin taron Umaru Musa Yar’adua da ke Abuja.

Ya ci gaba da cewa, bangaren ilimi na daga cikin bangaren da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci tun bayan hawansa karagar shugabacin kasar nan a shekarar 1999.

Cibiyar, wadda budadiyar jami’ar ta bude, an sanya mata sunan tsohon shugaban kasar ne bisa gudunmawar da ya bai wa fannin ilimi a fadin kasar nan, wanda kuma shi ya inganta jami’ar.

A cikin jawabin da ya gabatar mai taken, kalubalen shugabanci, da gudanar da mulki ga ci gaban Nijeriya, ya yi dogon fashin baki dangane da bambancin da ke tsakanin kyakkyawan shugabanci da ci gaba a kowanne mataki na shugabanci.

Tsohon shugaban, wanda dalibi ne a matakin digirin digir-gir a jami’ar, ya yi godiya ga hukumar jami’ar da suka karramashi ta sanya wa cibiyar sunansa.

A nashi bangaren, uban taro, sannan tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya yaba da yadda tshohon shugaban kasa ya gabatar da laccar da irin binciken da ya gudanar a kai, inda ya ce duk wani da zai gabatar da jawabi makamancin haka to, sai dai ya biyo bayan shi.

John Mahama ya kara da cewa, ya kamata Nijeriya ta yi tunani bisa hakkin da ya rataya a wuyanta na kula da kasashe da ke karkashinta na yammacin Afrika domin samun nasarar bunkasa a tattalin arzikin ta kamar na sauran kasashen duniya.

Da ya ke jawabin maraba ga mahalarta taron, shugaban budadiyar jami’ar, Farfesa Abdullah Uba Adamu, ya ce  dalilai da dama ne suka tabbatar da cancantar bude wannan cibiya da sunan tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Daga cikin dalilan da ya lissafa ya ce, kokarinsa na kawar da rashawa a kasar nan ne ya sa ya kirkiro hukumomin da ke yaki da almundahanar kudade da ayyukan rashin gaskiya, irin su ICPC da EFCC. 

Ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na dalibi a matakin digirin digirgir a wannan jami’a, yana gab da kammala bincikensa, sannan ya yaba masa bisa bayyana matsayar da ya yanke na neman ci gaba da karatunshi.

Ya ce, NOUN ce jami’a ta farko da suka taba yin dalibi shugaban kasa, a lokacin da ya ke karatunsa na digiri na biyu, kafin saukarsa a mulki a 2007.

Shugaban jami’ar ya kara da cewa, tun da aka bude jami’ar take samun ci gaba, wanda yanzu suke da dalibai da ke kan karatunsu sama da 300,000 a fadin jihohi 36 na kasar nan har da babban birnin tarayya, Abuja.

Taron ya samu halartar baki daga ciki da wajen kasar nan, wadanda suka hada da malaman jami’o’i, ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, ‘yan jaridu da baki da dama.
©Zuma Times Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button