Uncategorized

Tun bayan komawar shugaba Muhammadu buhari birnin london a ranar lahadi 07/05/2017, har zuwa wannan rana Hoto guda dayane kawai aka saki wanda ke nuna shugaban a birnin london.Kamar yadda labari yake zuwa mana jikin Baba Buhari yana kara yin sauki Alhamdulillah. …..

Hotuna masu yawa suna yawo akan dandalin sadarwar zamani na Facebook da twitter wadanda ake cewa Baba ne tare da likita ko wasu mutane na daban…. 

Maganar gaskiya dukkan hotunan da ake sakawa ba sabbin hotuna bane,  wannan guda dayan shi kadaine kawqi wanda aka saki amma dai jikin baba yana kara ingantuwa Alhamdulillah. ……

Soyayya da damuwar da ake da ita akan shugaba buhari hakan ne ke sanyawa al,umma su dinga yadda da hotunan, kuma hakan ne ke sanyawa jaridun karya da marubatan karya suke amfani da damar wajen yawo da hankalin masoya baba……

SHAWARA…..

A matsayinka na masoyin shugaba Muhammadu buhari idan har kana bukatar samun ingantatten hoto ko labari akan shugaba buhari to zaifi kyau ka dinga ziyartar Shafin masu temaka masa a hanyar sadarwa irin su Garba Shehu, Femi Adesina, da kuma Bashir Ahmad anan ne kawai zaku samu labarin mai inganci……

Haka akwai marubutan Baba Buhari masu zaman kansu irin su Buhari Sallau, Biyora da sauransu wadanda tabbas in har kaga sun saka hoto ko labari akan Shugaba buhari to in sha Allah gaskiya ne……….

Masoya Baba Addua zamu cigaba da gudanarwa kamar yadda muka saba…. Baba zai dawo in sha Allah nan ba dadewa ba………

Sources:Rabiu biyora
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button