Uncategorized

Tarihi Zai Iya Mai-maita Kansa A Masarautar Kanon Dabo

Na tab’ayin Wannan Rubutun Cewa, Kafin Kakana Ya rasu na ta6a tambayarsa dalilin da yasa aka sauke Sarki Sanusi (Kakan Sanusi Lamido Sanusi) daga kan Mulkinsa, Sai ya bani labari daga farko har zuwa k’arshe.

Yadda abin ya faru har aka sauke sarki Sanusi (Mahaifin mahaifin Sanusi Lamido) Shine, A Lokacin Sa Ahmad Bello Sardaunan sokoto shine firimiyan Jahar arewa sai ya aika wa sarkin Kano Sa Alh. Sanusi Bayaro cewa ya shirya hawan daba domin zai kawo masa ziyarar gani da ido shi da shugaban Nijar na wancen lokacin Alh. Jori Hammani.

Kasan cewa Sarki Sanusi mai kulane da biyayya nan take ya saka mahaya suka shirya dawaki aka share gari aka kawata gari (garin kano yayi kyau sosai).

Bayan an shirya wuri tsaf Sarki Sanusi ya fito ya samu wuri a cikin rumfar manyan baki ya zauna yana jiran zuwan Sardauna Jikan shehu tare da abokin rakiyarsa Jori Dan Hammani da tare da mutanen su. A wancen lokacin Su Sa Ahmad Bello tafiyar mota ce sukayo kasan cewa jirgi bai wadatu sosai ba.

Tun karfe daya na rana Sarki Sanusi ke jiran baki har karfe biyar na yamma amman shiru ba su zo ba (babu ko alamarsu).

Sai sarki ya tashi zai shiga gida har ya kai bakin kofa bai kai ga shiga ba sai ga bakin da yake jira (su Sa Ahmad Bello), sun iso sarki zai juyo ya dawo sai wani d’aya daga cikin fadawansa yace “HATTARA DAI GIWA BATA KWANA”, Nan take Sarki Sanusi ya fasa Juyowa ya shige gidansa.

Su Sardauna suka yita jira shiru sarki bai fito ba har suka gaji da jiransa amma bai fito ba. Nan Jori Dan Hammani yace wa Sardauna, Shin da kai da shi wa ke karkashin wuni? Sai Sardauna yace, “shike kasa dani.”

Nan fa Jori ‘dan Hammani, yace to ka cire shi ka huta da irin wannan girman kan nashi. Sardauna yace masa ba damuwa zan duba in gani nan suka wuce zuwa Kaduna inda gidan Sardauna yake.

Bayan isarsu Kaduna da ‘yan kwanakki sai Sardauna ya kafa kwamitin bincike ya turo kano akan abinciki yadda sarki ya kashe kudaden da gwamnati ta turo wa masarautar Kano.

Bayan gama binciken ne aka samu ‘yan kura kurai daga wajen Sarki Sa Sanusi domin kuwa an samu salwantar wasu daga cikin kudaden. Ganin haka Sarki Sanusi ya fahimci me sardauna yake nufi nan take ya yi Murabus.

Bayan yin murabus dinsa ne Sarkin Kano Muhammadu Inuwa ya hau mulki yayi wata bakwai saman mulkin.

Daga nan ne Sardauna ya turo da cewa a zabi wanda zai hau karagar mulkin, a nan ne aka mika sunan Alh. Ado bayero a matsayin Sarkin kano.

Bayan rasuwar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero Allah ya damka amanar ragamar mulkin kano hannun Muhammadu Sunusi II, wanda jika ne a wurin Marigayi Sarki Muhammadu Sanusi mai murabus.

Tun bayan darewar Muhammad Sanusi II kan karagar mulkin Kano aka fara jin sabon yunkurin sake salon tafiyar da fadar Kano, ciki har da sake salon zaman fada.

Haka kuma Sarki Sanusi II ya kalubalanci gwamnatin jihar Kano akan jirgin kasa da take shirin samarwa a jihar, ta hanyar ciyo bashi daga kasar Chana. Sarkin ya ce, wannan jirgi ba zai amfani rayuwar talaka ba ko kadan, sai dai ma barin jiha da za a yi da tulin bashi.

Haka kuma Sarkin, ya kalubalanci gwamnan gwamnonin APC gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari dangane da kalaman da yayi na cewa zunubbai ne suka janyo barkewar Sankarau a jihar Zamfara.

To Tun bayan wadannan kalamai da sarkin yayi a garin Kaduna, sai lamurran suka dauki dumi tare da sauya salo. Domin kuwa wayannan Kalamai ba karamin Batawa Gwamnatocin APC rai yayi ba.

Inda cikin Gaggawa wasu daga cikin gwamnonin arewa Suka kira zama a birnin Guanzhou da ke k’asar Chana Inda suka kira wannan zama da zaman yadda za’a bullowa Sarki Sanusi.

A bangare daya kuma suka ce sunje ne domin yin taron cibiyar masu zuba hannun jari a kasar.

A zaman nasu gwamnonin suka ce, matukar gwamnatin jihar Kano ta zuba ido ba tare da daukan kwakkwaran mataki akan sarkin ba, haka zai yi ta sakin baki ya na sukarsu da ajandodinsu. A k’arshe ma zai iya sanya talakawa yin bore.

Zaman da akayi da Wasu daga cikin Gwamnonin arewa, cikinsu har da Gwamna Ganduje (gwamnan kano), sun hadu domin daukar mataki mai kwari akan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Inda da yawan gwamnonin suka bukaci da a tsige sarki Muhammadu Sanusi.

Wasu daga cikin gwamnoni kuma suka bukaci da kar a tafi kai-tsaye ga tsige shi, a fara bin matakin bincikar asusun masarautar da yanayin yadda aka tafiyar da kudaden ciki, kafin a kai ga matakin tsigewa.

Ana haka kwatsam bayan dawowar gwamnonin daga Chana sai hukumar sauraron koke da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bude babin bincikar asusun masarautar jihar Kano, bisa zargin masarautar da ake yi da tarwatsa biliyoyin kudaden da ta gada a cikin dan kankanin lokaci.

Inda kai tsaye hukumar ta aika da sammaci ga ma’aji da sakataren masarautar ta Kano, domin su halarta a gaban hukumar don yin karin haske kan yadda aka kashe naira biliyan 4.

Hummm kowa dai munafuki ne, bayan wannan sammaci sai hukumar sauraron korafi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta nemi izinin gwamnan jihar, akan za ta binciki wannan lamari.

Suka ce akwai hadarin gaske a barshi ba tare da bincike ba. Wanda ba tare da wata-wata ba
gwamnan ya amince da a gudanar da binciken. (Alhali kuma duk bakinsu daya).

Haka kuwa akayi Ma’ajin masarautar ta kano wanda shi ne kuma Walin Kano, Alhaji Bashir Wali ya bayyana a gabansu ya musu bayani dalla-dalla (na yanda aka kashe kuddin). Bayan bayanin da ma’ajin yayi sak hukumar ta nuna sam bata gamsu da ba
yanin na Shi ba.


Shine nake tunanin Anya ba tarihi ne Zai mai-maita kansa ba ???

©Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon-05-2017

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button