Sarkin Kano Zai Sake Shiga Chakwakiya
SARKIN KANO ZAI SAKE SHIGA CHAKWAKIYA
Yanzu haka an kafa kwamitin binciken sarkin Kano Muhammad Sanusi Lamido Sanusi kan tuhumar shi da ake yi da wasu batutuwa 8 ciki harda cin mutuncin masarauta, rashin iya magana, da yin kage ga yan siyasa da sauran su.
Bayan haka Sarki Sanusi yana fuskantar bincike kan batun makudan kudade da yawan su ya kai nera biliyan hudu 4b daya gada daga tsohuwar masarautar margayi Ado.
Dan-majalisar Jihar kano Ibrahim Gama shiya gabatar da kudirin a gaban majalisar kuma ya bukaci a tuhumi Sarki Sanusi akan batun, take kakakin majalisar Alhassan Rurum ya shirya kwamitin mutane bakwai dan binciken batun.
Yan-majalisun da ke ciki kwamitin sun hadar da Abdul Madari (Ajingi) Baffa Babba Dan’agundi (Kano Municipal) Kabirg Dachi (Kiru).
Idan baku manta ba a bayabayannan Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El’rufa’i da wasu daga cikin gwamnonin Arewa suka shiga suka fita wajen ganin sun sulhunta tsakanin Sarki Sanusi da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Rahoto :AMINIYA