Rundunar sojin Najeriya ta kama ‘Yan Boko Haram 126
– Rundunar sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri, ta ce ta kame wasu mutane 126 da suke zargin cewa ‘yan kungiyar Boko Haram ne
– Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janal Lucky Irabor, shine ya shaidawa manema labarai hakan lokacin da yake jawabin ban kwana ga manema labarai a garin Maiduguri
-An kama ‘Daya daga cikin mutanen dauke da jakar ajiye kudi ta ‘daya daga cikin sojojin da aka kashe
Rundunar sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole, ta ce ta kama wasu mutane 126 da ake zargin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne, sannan kuma su ake zargi da kai hari garin Sabon Gari dake hanyar Biu.
Kwamandan rundunar sojin ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janal Lucky Irabor, ne ya shaidawa manema labarai hakan a yayinda yake jawabin ban kwana ga manema labarai a babban birnin jihar Borno.
Irabor, ya ce idan aka waiwaya baya, kimanin makonni biyu da suka gabata wasu da ake zargin ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari Sabon Gari, inda suka hallaka wasu jami’an sojin Najeriya guda shidda tare da jiwa wasu da dama raunuka, da kuma kwashe wasu makamai wanda yanzu haka an samu nasarar kwato wasu daga cikin makama.
Ya kara da cewa suna samun bayanai na sirri da ke nuni da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan Boko Haram din da suka kai hari Sabon Gari na shirin kai sabon hari a garin Dambua, inda wasu daga cikinsu suka shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Dambua suka saje da mutane. Amma rundunar sojin ta samu babban nasara a kansu.
Daya daga cikin mutanen da aka mutanen da aka kama an same shi da jakar ajiye kudi ta daya daga cikin sojojin da aka kashe, tare da katin shaidar sojan da katin zarar kudi dukkanninsu mallamar sojan tare da mutumin da aka kame.
Irabor, ya ce ko cikin kwanaki biyu da suka gabata an sami matsalar tashin bama-bamai a garin Kwandiga, inda wasu ‘yan kunar bakin wake uku suka shiga suka tayar da bama-baman da ke jikinsu suka hallaka mutum guda.
A wani al’amari makamacin haka, NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace gwamnatin jihar ta dakatar da shawarar da ta dauka na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira saboda burbudin aiyukkan Boko Haram da har yanzu jihar ke dan fama da su.
Ya fadi hakan ne a bukin mika wa jihar gudunmuwar wasu gine-gine da gidauniyar ‘Victims Support Fund VSF’ ta yi a garin Bama ranar Talata.
Gwamnan ya ce gwamnati ta amince da shawarar dakatar rufe sansanonin ne kamar yadda ada ta shirya saboda kira da shawarwarin da jami’an tsaro suka bata da ta dada jinkirtawa tukuna.
Hukumar sojin Najeriya na ci gaba da yakar Boko Haram
©Naij.com