Uncategorized

Neman Tsige Sarkin Kano Zai Taba Darajar Sarautu – Bafarawa

NEMAN TSIGE SARKIN KANO ZAI TABA DARAJAR SARAUTU- Bafarawa

Daga Ibrahim Baba Suleiman 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce daukar sabbin matakai kan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bayan sulhun Kaduna ba daidai ba ne.

Bafarawa da ke magana da manema labaru a Abuja, ya ce karin mataki ko ma neman kwabe Sarkin zai rage darajar sarauta ne da hadin kan arewa.

Yayin da Bafarawa ke ganin sulhu ne mafi a’ala, ya ce ba wai ya na kare Sarkin ba ne, amma ya na kare kujerar sarautar ce da ke da tasiri wajen hadin kan al’umma.

Sakkwato Birnin Shehu 
12th May, 2017

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button