Uncategorized

Kun san likitan da yake duba mutum 750,000 shi kadai?An karrama likitan da yake duba mutum 750,000 shi kadai

An karrama wani likita, wanda shi kadai yake duba lafiyar mutane fiye da 750,000 domin ya rika yin aikin fida fiye da 1,000 a ko wacce shekara a kasar Sudan.

Likita Tom Catena, mai shekara 53 da haihuwa, mabiyin darikar katolika ne daga birnin New York, an karrama shi da lambar girma ta Tallafa wa Bil Adama ta Aurora.
Yayi aiki a Sudan na tsawon shekara fiye da 10, a lokacin yakin da aka fafata tsakanin gwamnati da mayaka ‘yan tawaye.

A kalamansa a lokacin bikin, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka a warware rikicin da ke hana samar da taimakon jin kai ga al’ummar yankin.

Dokta Catena shi ne likita daya tilo a yankin tsaunukan Nuba, inda yaki tsakanin sojojin gwamnatin shugaba Omar al-Bashir da ‘yan tawayen kungiyar SPLM-Arewa ya ki ci, ya ki cinyewa.

An sha yaba masa domin kokarin da ya yi na shawo kan matsalolin rashin kayan aiki da magunguna a asibitin katolika na Mother of Mercy da ke tsaunukan Nuba, duk da aikinsa na duba wadanda suka jikkata saboda hare-haren da aka rika kai wa yankin.

“Gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen suna takaddama tsakaninsu game da wanda zai rika shigar da kayan agaji”, in ji Dokta Catena.

“Dole mu yi allurar hankali.”
Dokta Catena ya sanar da wadanda suka halarci bikin cewa gwamnatin kasar na son tabbatar da ikonta a kan shige da fice na kayan agajin.
“‘Yan adawa na ganin akwai maganin hana haihuwa daga bangaren gwamnatin Sudan. Saboda haka suka fi son taimako daga Sudan ta Kudu mai makwabtaka da su.

Tun a shekara ta 2007 yake aiki a Sudan, inda ya rika duba masu raunuka da suka samu daga harbi. Ya rika karbar haihuwa da kuma yanke kafafuwa.

Dan wasan fim George Clooney ne ya mika wa likitan lambar yabon. “Dukkanmu muna da rawar da za mu taka domin wannan batun da ya shafi duniya. Muna da hakki a kanmu, dukkanmu”, in ji Mista Clooney.
“Dole mu taimaka.”
Sauran wadanda aka karrama sun hada da wani likitan hakora wanda ya yi aikin tiyatarsa ta farko lokacin yakin Siriya ta hanyar aikawa da hotunan masu bukatar aikin ga wasu kwararun likitocin da ke kasashen wajen ta hanyar shafukan zumunta.

Muhammad Darwish dan shekara 26 yana daya daga cikin likitoci uku da suka rage a garin Madaya, garin da a lokacin an yi masa kofar rago.

“Ba zan manta wannan batun ba har tsawon rayuwata”, in ji shi.
“Ka zama ka sami kanka a halin da dole ka yarda wani wanda ba shi da isasshen horo ya yi tiyata a kan danka, kuma nima in yarda da hakan har in yanka cikin mutum mai rai a bisa tebur, lallai wannan lamarin bai kamata ma ya faru ba.
An yi nasara a aikin.

Ita ma Fartuun Adan wata mai rajin kare hakkin dan adam ce da ke birnin Mogadishu ta kasar Somaliya tana cikin wadanda aka karrama.

Mayaka sun kashe mijinta a shekara ta 1996 kuma tun lokacin take aikin taimaka wa kananan yaran da yakin ya rutsa da su.
Ta kafa cibiyar farko domin tallafa wa matan da aka yi wa fyade a Mogadishu.

Sai kuma Jamila Afghani daga Kabul, wacce take fafutukar ganin malaman addini sun mayar da hankulansu ga batun hakkokin mata.

“Idan ka ilmantar da mace daya, to ka ilmantar da iyali gaba daya ne. Kowa na amfana da iliminsu”, in ji ta.

Shi kuma Dokta Denis Mukwege daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya taimaka wa fiye da mutane 50,000 a kan batutuwan cin zarafin jama’ai a kasar da aka lakaba wa sunan shalkwatar fyade ta duniya.

Rahoto Daga bbchausa_com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA