Sports

Ko tikiti 9,500 zai ishi magoya bayan Man United?


Ƙungiyar Manchester United ba za ta samu sama da tikiti 9,500 ba, na shiga wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Europa, a filin wasa na Friends Arena da ke daukar mutum 50,000.

Ƙungiyar dai za ta kara da Ajax, wacce ita ma za ta samu tikitin daidai da na United din, a wasan da za su fafata ranar 24 ga watan maris.

Sauran tikitin za a sayar da shi ne ga jama’a, da kuma ƙungiyoyi, da ‘yan kasuwa, da manema labarai, da kamfanoni masu zaman kansu.
Ba za a tantance magoya bayan da ba su da tikiti ba, don shiga filin wasan.

Magoya bayan Utd ɗin da za su iya samun tikitin wannan wasa, su ne waɗanda ke da tikitin wasannin ƙungiyar a wannan kaka, waɗanda suka halarci dukkan wasan da ta yi a wannan kakar, da wadanda ke da tikitin ƙungiyar wadanda suka nemi samun tikitin wasan da ƙungiyar ta yi a waje a gasar cikin shekara biyu da ta gabata.

Duk da wannan sharaɗi, ƙungiyar na tsammanin samun masu neman tikitin fiye da tikitin da aka ware mata.
A shekarar da ta gabata dai Liverpool da Sevilla sun samu tikiti 10,236 ko wannensu, a filin wasan da ke ɗaukar mutum 35,000 na St Jakob-Park, da ke birnin Basel na kasar Switzerland.

Rahoto :bbcahusa.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button