An karanta wasikar shugaba Buhari dazu a gaban Majalisa
Bukola Saraki ne ya karanta takardar da shugaban kasa ya aiko
Shugaban kasar bai fadi ranar da zai dawo Najeriya ba
Dazu-dazu Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya karanta wasikar da shugaban kasa Buhari ya aiko zuwa ga Majalisar game da tafiyar sa zuwa Landan domin ganin Likita. Shugaban kasar bai bayyana lokacin da zai dawo ba a takardar.
A takardar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mataimakin sa zai zama mukaddashin shugaban kasar. Farfesa Yemi Osinbajo ne zai koma rike ragamar kasar har lokacin da Ubangiji yayi shugaba Buhari ya dawo.
Bashir Ahmad ya maidawa Dionne Searcey ta Jaridar NY Times martani game da rashin lafiyar Buhari. Searcey tace ana zaman dar-dar a Najeriya saboda gibin da aka bari. Bashir ya tuna mata cewa Osinbajo na rike da madafan iko.
sources: naij.com/hausa