Kannywood

Rahma Sadau Ta Maka Nafisa Abdullahi A Kotu.


Jaruma Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi a kotu. wanda tace tana neman hakin ta agun Nafisa Abdullahi.

Wanda tace ta hana ta kudin ta har naira dubu tamanin da tara. Wanda Rahma Sadau taba Nafisa Abdullahi domin ta fito acikin fim din ta maisuna RARIYA. Amma har aka gama yin fim din Nafisa Abdullahi bata fito koda sau daya acikin fim din ba.
Anayin wannan sharia’a ne akotun Nomans land dake jihar Kano.

Majiyar mu ta kotu Sadiya Rk Panshekara ta ruwaito mana cewa: za’aci gaba da sauraron shar’ar ranar litinin.

Kamar yadda majiyarmu ta tattaro cewa a zantawar da wakiliyar mu tayi da wadda akeyin kara Nafisa Abdullahi sai jarumar tace: ni ba wasu kudi da Rahma ta bani dan nayi mata fim.

Abinda nasani shine, tace tanaso na fito acikin fim din ta maisuna RARIYA nace zan fito amma sabida wasu dalilai ban fito ba, amma ni ba wasu kudi da ta bani. Inji Nafisa Abdullahi.
To, mu dai aikin mu bibiya. zamu ci gaba da kawo maku yanda shari’ar take tafiya.

® Naij Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button