Uncategorized

Kun san wanda ya mallaki kuɗin da EFCC ta gano a Lagos?

Batun makudan kudin da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta gano a wani gida a birnin Lagos a farkon wannan makon, na cigaba da jan hankalin ‘yan kasar.

Kudaden, wadanda suka kai N13b da EFCC ta ce jami’anta sun gano a unguwar Ikoyi bayan wani ya tsegunta musu cewa an jigbe su a gidan a nau’in dala da fam da kuma naira, sun sanya ‘yan kasar na ta fadin albarkacin bakinsu, musamman a wannan lokacin da ake cikin matsin tattalin arziki.
Sai dai babban abin da ya fi jan hankalin ‘yan Najeriya shi ne yadda aka ‘rasa’ masu wadannan makudan kudin.

Jim kadan bayan EFCC ta gano kudin ne dai, wasu rahotanni suka ce babbar jami’ar kamfanin mai na NNPC wacce aka kora a farkon mako, Mrs Esther Nnamdi-Ogbue ce ta mallake su.

Sai dai nan da nan ta fitar da sanarwar da take nisanta kanta da su.

Shi ma tsohon Shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, wanda aka ce gidan da aka kama kudaden nasa ne, ya ce ba shi da alaka da kudin.

Ahmadu Mu’azu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce gidan nasa ne amma ya sayar da shi kamar yadda ya saba, kasancewarsa dan kasuwar gidaje tun ma kafin ya shiga harkokin siyasa.

Ba su da uba

Tuni dai wata babbar kotun tarayya da ke birnin Lagos ta bayar da umarni a mika kudin ga gwamnatin tarayya a matsayin wucin gadi, kafin wani ya fito ya ce nasa ne sai a dauki mataki na gaba.

Hakan ne ya sanya ‘yan kasar da dama, musamman a shafukan sada zumunta, ke yin kira ga EFCC ta tuhumi mutumin da ya tsegunta mata inda kudin suke.

Wani fitaccen mai sharhi a shafukan na zumunta, Japeth Omojuwa, ya ce babu yadda za a yi mutumin da ya tsegunta wa EFCC wadannan makudan kudade ya kasa sanin mutumin da ya mallake su.

Hasalima, a cewarsa, ta kwana gidan sauki tunda EFCC ta ce wanda ya tsegunta mata inda kudin suke, ya ce wata mata ce sanye ka tufafi marasa kyau ta rika ajiye kudaden.

Kudinmu ne

Sai dai wasu rahotanni na cewa kudin na hukumar tsaron ciki ce, National Intelligence Agency, NIA, wadanda tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ba ta domin ta gudanar da wasu ayyukan tsaro cikin sirri.

A cewar rahotannin, tun ma lokacin da jami’an EFCC suka je gidan, shugaban NIA ya buga wa shugaban EFCC waya inda ya sanar da shi cewa kudin hukumar ne, amma Ibrahim Magu ya yi burus da hakan, inda ya bukaci jami’ansa su kama kudin.

Na yi kokarin jin gaskiya ko akasin wadannan rahotanni daga kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, amma bai amsa kiran wayar da na yi masa ba, sannan bai aiko min da amsar sakon da na aike masa ba.

Amma wani abu da ya kara cakuda wannan batu shi ne zargin da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi cewa kudin na jiharsa ne wanda tsohon gwamnan jihar kuma ministan sufuri na yanzu, Rotimi Amaechi ya sace a lokacin da yake mulki.

A wata hira da ya yi da manema labarai ranar Juma’a da daddare a birnin Fatakwal, Gwamna Wike ya ce kudin, wani bangare ne na kudin gas din da aka sayar lokacin mulkin Amaechi amma ya sace su.

Sai dai tun ma kafin Mr Wike ya yi wannan zargi, mai magana da yawun Mr Amaechi, David Iyofor, ya musanta cewa kudin na mai gidansa ne bayan wani mai magana da yawun gwamnan jihar Ekiti ya zargi tsohon gwamnan da mallakar kudin, yana mai cewa sokiburutsu ne kawai.

Mr Iyofor, a wata hira da muka yi da shi ta wayar tarho, ya kara da cewa za su yi wa manema labarai karin bayani kan batun nan ba da dadewa ba.

Da alama dai za a ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan wadannan kudade har lokacin da kotu za ta yanke hukunci a kan batun.

Daga bbchausa.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button