Uncategorized

Facebook zai rufe shafukan batsa


Kamfanin Facebook ya dauki sabon mataki don hana yan ta’adda yada batsa a shafin.

Shafin sada zumuntar na zamani ya ce zai yi iya kokarinsa wajen hana yada ko saka hotunan mutane ba tare da izininsu ba.

Matakin ya shafi manhajojin Facebook da Messenger da kuma Instagram amma bai shafi WhatsApp ba.
Masu fafutika na maraba da daukar wannan mataki.

Laura Higgins, wacce ta samar da layin waya na agaji kan shafukan batsa na kasar Amurka ta ce, wannan babban mataki ne.

“Sau da yawa hotunan da aka hana sa wa a shafukan sada zumunta na wani bangare na irin halin da ake ciki na yau da kullum, inda wani yake kokarin cimma wata manufa daga makusanta da abokai,” in ji ta.
Ta kara da cewa “Daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta shi ne a hana mutane kara yada abin da ya kunsa.”

‘Mataki na farko’

Shafin Facebook ba farutar hotunan batsa yake ba, amma ya dogara a kan masu amfani da shi da suke yada abin da ke kunshe ta hanyar shafukan rahotanninta.

Tawagar jama’ar da ke aikinsa za su yi hukunci a kan ko yadawar ta cancanta, abubuwan da ake la’akari da su sun hada da ko ayyukan batsa da aka nuna, sannan a duba mutumin da ya yi korafi.

Idan an tabbatar da hoton na batsa ne, to za a cire shi kuma a rufe shafin — wannan doka ce da ake shirin aiwatarwa.

An saka tsaro a shafukan don tabbatar da duk wanda ya yi yunkurin yada wani hoto an rufe shafin ba tare da duba ko la’akari da bukatar mutum ba.

Na’urar ta yi daidai da wanda shafin Facebook ke amfani da shi da kuma sauran abubuwan da suke hana yada hotunan cin zarafin yara.
Wata mai kula da ingancin shafin Facebook, Antigone Davis ta shaida wa BBC cewa, “Kodayaushe muna kokarin mu samar da kayayyaki da zai bayar da dama kuma ya zama a bayyane a gurinmu cewa wannnan matsalar da take faruwa a yankuna da dama na haddasa cutarwa ta musamman”.

Wannan ne mataki na farko, kuma za mu yi kokarin samar da abubuwan fasaha mu gani idan zamu iya hana yadawa, in ji ta..
Ms Davis ta kara da cewa, Facebook zai duba yiwuwar yadda za a fuskanci matsalar a WhatsApp nan gaba.

Duk da haka, manhajar na amfani da na’urar takaitawa a boye, wacce ta sa Facebook ba zai iya ganin abubuwan da masu amfani da shafin suke turawa junansu ba.
Mummunan hari

Ms Higgins ta ce kungiyarta na aiki a kan rikice-rikicen da suka shafi batsa sama da 6,200 tun a shekarar 2015, inda ta ambaci adadin a matsayin babbar matsala.
Ta ce sadaukar da shafukan batsa ta zama babbar matsala, inda ta kara da cewa tana fata sauran kamfanonin shafukan sada zumunta za su bi sawun Facebook.     Sources:Bbchausa.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button