Hausa Musics

Bikin Nura M Inuwa Ya Tayar Da Zaune Tsaye

BIKIN NURA M INUWA YA TAYAR DA ZAUNE TSAYE.
2142017.
.
Kamar yanda muka sanar daku a wannan dandali cewa mawaki Nura M Inuwa zai angonce da amaryarsa yar garin katsina, to anan ana ci gaba da shagulgula kafin ranar dauren aure. Amma da yake bikin na manyane kun san ba’a rasa ‘yan kunji-kunji ataron biki.
.
To shima bikin Nura ya tayar da zaune tsaye.
Domin jarumai ne suke ta musayar yawu da fadi tashi akan yanda zasu birge jama’a a bikin Nura. duk wanda yake da budurwa a kannywood to wannan lokacin kudinsa sun shiga uku.
Adam A Zango yana daga sahun manyan abokan Nura M Inuwa. Wanda duk cikin abokan Nura ba wanda yake watsi da baragaza da naira kamar Adam A Zango.
Abin burgewa da sha’awa shine, Ali Nuhu da shi ake ta gudanar da shagalin bikin auren Nura M Inuwa, wanda abaya wasu sunata zargin ba’a ga maciji tsakanin su.
Acikin mata kuwa Nafisa Abdullahi da Fati Washa sune amara kirjin biki.
Waka da yawa sun yi wakokin auren Nura M Inuwa amma Umar M Shareef shine ja gaban su.
Allah Yasa Hakane Yafi Alkairee

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button