Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba
Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba
A ranar Juma’a ce aka fitar da wani shahararren fim ɗin Bollywood a kasar Indiya mai suna Bahubali kashi na biyu.
Fim ɗin Bahubali na 2 tun kafin fitarsa, ya ja hankalin mutane ciki har da wadanda ba su damu da kallon fina-finan Indiya ba.
Tun a ranar Alhamis, aka fara nuna wannan fim a Amurka.
Shi ne irinsa na farko da aka kashe makudan kuɗaɗe wajen shirya shi, saboda haka ne a kusan ko’ina duniya ake maganarsa.
A Indiya kadai, za a nuna shi a Silimu sama da 6,500 cikin manyan yaruka daban-daban na kasar, babu wani fim da ya taɓa samun irin wannan tagomashi a tarihin Bollywood.
Fim ɗin, ci gaba ne daga Bahubali kashi na ɗaya, wanda ya fita a shekarar 2015, kuma ya samu karɓuwa sosai a duniyar fina-finai.
Sharhi, Aisha Shariff Baffa
Babban dalilin da ya sa Bahubali na biyu ya samu karɓuwa a wajen mutane shi ne yadda ya yi tsokaci cikin sha’anin masarauta.
Ya fito da irin kutungwila da maƙarƙashiyar da ke da alaƙa da neman mulki a wajen wasu. Bayan kashe wani sarki a fim ɗin na Bahubali, sai kuma ake yunƙurin kashe ɗansa.
Abin da mutane ke son gani a kashi na biyu shi ne, dalilin da ya sa babban na hannu daman sarkin, ya ci amanar sarki ta hanyar kisan gilla.
A Nijeriya, masu sha’awar fina-finan Indiya ba a bar su a baya ba, inda suka shiga sahun masu alla-alla su ga fitowar Bahubali na biyu da ke faɗin duniya don kashe kwarkwatar idanunsu a wannan fim.
Source :bbchausa.com