Aisha Aliyu Tsamiya, Umar M Shareef Da Ado Gwanja, Zasu Zo Sokoto Waje Yin Wasa
Aisha Aliyu Tsamiya, Umar M Shareef Da Ado Gwanja, Zasu Zo Sokoto Waje Yin Wasa.
Ina masoyan Aisha Tsamiya da masoyan Umar M. Sharif tare da masoyan Ado Gwanja, to Albishirinku.
Shahararriyar Yar Wasar Fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya, Shahararren Mawakin Hausa Umar M. Sharif tare da Shahararren Mawakin Hausa Ado Gwanja, za su zo Sokoto wajen yin Wasa.
Kungiyar Makaranta Mujallar Fim ta Kasa, itace ta shirya wannan wasar, wadda ba’a taba irin ta a Jahar Sokoto ba.
Za’ayi wasar ne kamar haka.
AISHA ALIYU TSAMIYA.
Zata yi wasa Ranar Assabar 29 April, 2017.
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare.
Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare.
UMAR M.SHARIF.
Zai tashi Wasar Ranar Lahadi 30 April, 2017.
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare.
Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare.
ADO ISAH GWANJA.
Zai tashi wasar a Ranar Attanin 01 May, 2017.
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare.
Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare.
Dukkan su zasu yi wasar ne a Ahmad Maigero open Theater, kusa da gidan Gwamnatin Jahar Sokoto.
Kudin shiga wajen wannan wasar kuwa, ba’a sanya su da yawa ba.
Daga Dan Shekara 18 zuwa sama zasu biya kudin shiga Naira Dari biyar Kacal #500.
Daga Dan Kasa da shekara 18 zuwa kasa, su kuma zasu biya Naira uku kacal #300.
Domin karin bayani, sai ku tuntubi wadannan Lambobi, kamar haka.
1. 08069661227.
2. 08069452044.
3. 08095874748.
4. 08034543434.
5. 07035967561.
6. 08030836649.
SANARWA DAGA.
Kungiyar Makaranta Mujallar Fim Ta kasa Reshen Jahar Sokoto.