Uncategorized

Paul Pogba Ya Kafa Tarihin A Gasar Premier League Wanda Babu Wanda Ya kafa

Pogba ya kafa tarihi a gasar Premier


Dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United Paul Pogba ya zama dan wasa na farko a kakar wasan Premier ta kasar Ingila a bana, da ya samu nasarar rarraba kwallo (passing turance) har sama da 1000 yayin murzawa kungiyarsa leda.
Wani sakamakon bincike da masana masu bibiyar kwallon kafar Ingila, ya nuna cewa, Pogba ya rarraba kwalo har sau 1029 yayin karawa da abokan hamayya.

Zalika matakin kwarewar Pogba wajen bada kwallo yayin wasa ya kai matakin kashi 83.05 cikin dari.
Jordan Henderson na kungiyar Liverpool ke biyewa Pogba da samun nasarar rarraba kwallo har sau 987 yayin yi wa kungiyarsa wasa.
Mesut Ozil na Arsenal ke a matsayi na uku da yiwa kwallon kafa rabo na dalla dalla tsakanin ‘yan wasa yayin karawa da abokan hamayya sau 954.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button