Uncategorized

Musulunci A Mahangar Makiya -Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Musulunci A Mahangar Makiya

A kullum makiyan musulunci sun sawo mu a gaba,
 kamar masu laifi,  da tuhumai tuhumai,  akan
addninmu da al’adummu,
Suna tuhumar addininmu da cewa,  akwai abubuwa
goma da muke yi na takurawa mata,  Abin yana damun mu, amma Hanyoyin da ake bi
wajan magance , matsalar sai ake kokarin a biye
musu.

Masu Yin haka sun kasu kashi biyu, masu niyya mai
kyau, amma basu bi hanya mai kyau ba, wajan
kalubalantar wadananan akidu na turawa.

Na biyu masu Mummmunar aniya, Wadanda suke
so abiya wa wadannan turawa bukata, ta yadda
zamu karbi wadananan akidu na su na sukar
addini yadda suke bukata.

Abubuwan sune kamar haka:
Na daya maganar gado da ake bawa mata daya a bawa maza biyu.

a wasu guraran.

Na biyu kaciyar mata.

Na uku saka hijabi da nikab.

Na hudu shigar mata harkokin siyasa da
shugabanci.

Na biyar hukuncin kulle da neman izni kafin fita.
Na shida shekarun aure da auran wuri .

Na bakwai Maganar duka.

Na takwas auran mata fiye da daya.

Na tara AURAN DOLE .

Na goma haihuwar y’ay’a da yawa.

Wadannan abubuwa duka muna da amsoshi gamsassu akansu.
A biyo mu domin jin matsayin
addini akan wadannan abubuwa yadda addinin yake kallonsu.
Ba yadda turawa da yan korensu suke Fassara su ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button