Zul-karnain Wanene Fitowa ta 2? – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo
Zul-karnain Wanene 2
A cikin ayoyin goma sha bakwai (17) da Allah ya labarta mana kissar Zul-kurain,wasu sifofi sun bayyana wadanda sune za su zama amsa game da tambayar “Wanene Zul-karnaini.” Ga su kamar haka:
1. Sarki ne mai kadaita Allah ,wanda kuma yayi imani da ranar lahira
2.Allah ya ba shi karfin mulki ,wanda ya ci garuwa masu yawa da yaki;
3.Allah ya bashi duk wani abu mai mulki yake bukatar samunsa a zamaninsa domin kafa mulkinsa, da tabbatar da adalci a kasa.
4. Ya kasance mai kira zuwa ga bautar Allah shi kadai da yaki da bautar wanin Allah .
5. Ya karade duniya da yawo, ya isa yammacin Duniya daga nan ya dawo ya danna yammacinta,inda har ya kai wajen da ya gina babbar ganowa tsakaninsu Yajuju da Majuju da sauran kabilu makotansu.
6. Yana karbar umarninsa ne t hanyar wahayi da ake yi masa kai-tsaye (idan shi Annabi ne) ko ta hanyar wani Annabi dake tare da shi a cikin sojojinsa.
Allah kasa mu dace ,Allah ya sakawa mallam da Alkhairi .karka manta dan uwana kayi share zuwa ga yan uwa musulmi domin ka samu ladah yada abun alkhairi
ku kasance da sadeeqmedia