Uncategorized

Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al’umma – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al’umma:

Wajibi ne shugaba ya zama mai kamewa daga taba dukiyar al’ummarsa.kada ya zama mai kwadayi akanta.Idan yana da wadatar dukiya ya yi musu aiki ba tare da ya karbi haraji daga hannunsa ba.Yin hakan yana daga cikar adalci da karamci da shugaba na kwarai zai nuna .Ka dubu Zul-karnaini yayin da jama’a suka yi masa tayin su biya shi lada,don ya yi musu ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju ,masu shigowa gari suna musu barna da ta’addanci. Sai ya nuna musu cewa,abin da Allah ya hore mishi ya ishe shi,ba sai ya karbi na hannunsu ba.

Don haka ya yi musu katanga mai karfi ta kare da narkakkiyar dalma,ba tare da sun biya ko kwabo ba,in banda ma’aikata da wasu kayan aiki da ya nema daga wajensu.Allah ya bamu labarin hakan inda yace ,(“suka ce,”Ya Zul-karnaini! lallai Yajuju da Majuju masu barna ne a bayan kasa,shin mu baka wani lada ka gina ganuwa tsakaninmu da su.”sai yace ,”Abin da ubangijina ya ba ni ya fi mini Alheri ,amma ku taimaka min da karfi don in sanya muku ganuwa ta kankare tsakaninku da su.”[Al-kahfi,94-95]

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button