Uncategorized

Tarihin Muhammad Auwal Abu Abdirahaman Albaniy Zaria[Rahamahullah]

Tarihin Muhammad Auwal Adam Abu Abdirrahaman Albaniy [Rahamahullah]Sunana: Muhammad Auwal
Sunan mahaifina :Adam
Sunan mahaifiyata: Saudah
Abu Abdirrahman shine Alkunyata
Albaniy shine laqabina

An haifeni a unguwar Muciya sabon garin Zaria a shekarar 1960.

Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi litattafan da akeyi a zaure na fiqhu dana Lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai mabanbanta a kasata Nigeria da kasashen waje inda na koyi Qur’ani da dukkan kira’o’insa, hadisi da musdalah dinsa, tafsiri da usul dinsa, harshen larabci da fannoninsa, fiqhu da usul da Qawa’id dinsa d.s.

Nayi makarantar firamare a sabon garin Zaria
Nayi sakandare a kwalejin barewa Zaria
Nayi Diploma akan:

Law

Computer science

Mass Communication

Hausa Language

Nayi Degree akan ICT

Nayi Masters akan Islamic studies

Ni Professional journalist ne

Ni Certified microsoft engineer ne

Ni Linguistic ne

Na karanci library science

Nayi programme na N+ akan Computer

Nayi Programme na A+ d.s

Ina da company wanda yake gabatar da ayyuka a fannoni dabam-dabam
Na karantar da litattafai kusan dari a rayuwata a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da laccoci dabam-dabam a gida Nigeria da kasashen ketare
Na fassara litattafai na musulunci masu yawa.

Nayi tahqiqin litattafai da dama
Na gina cibiya mai suna Darul-Hadeethissalafiyyah Zaria Nigeria (DHSN) wadda a karkashinta akwai makarantu kamar:

Albaniy science international Academy (pre-nursery, nursery, primary da secondary) na bangaren maza dana bangaren mata

Daaru Ibn Katheer Litahfeezil Qur’an
Sheikh Nasiruddeenil Albaniy College of Higher Islamic studies.

Na fara gina jami’a mai suna Albaniy University of Information and Communications Technology

Na fara gina gidan marayu

Na samar da inda zan gina asibiti

Na samar da inda zan gina gidan rediyo da talabijin.

Na samar da dakin karatu (library) domin anfanar malamai da daliban ilmi

Ni mutum ne mai son cigaban al’ummata ta hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allah (saw) shine mai gidana
Banayin sassauci ko daga kafa akan duk abinda ya sabawa Qur’ani da sunnah a bisa manhajin magabata na kwarai, amma ina yin hakan tare da duba yanayi, wuri da kuma halayen mutane
Daga cikin sana’o’ina akwai:

Dinki

Kanikancin computer (computer engineer)

Mashawarci a harkar computer (computer consultant)

Computer networking

Aikin jarida

Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce d.s

Duk abinda na assasa a rayuwata da kudina na samar dasu domin ban dogara da kowa ba bayan Allah Mahaliccina, sannan sai sana’o’in da nakeyi
Nayi waqafin abubuwa dana assasa baki dayansu gareni domin anfanar al’ummar musulmi

Babban manufata shine sharewa musulmai hawaye game da matsalolin da suke fama dasu na addini da rayuwa a fannoni daban-daban a karkashin mahanga na addinin musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu indawo duniya in bayyanasu ba! Amma Ubangijinmu yana nan a madakata yana jiranmu a inda ranar Alkiyamah zan shako wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allah Sarkin sarakuna ince Ya tambayesu don me yasa suka kashe ni….?

Ina rokon Allah Yajikaina
Yayi mini rahma
Ya yafe mini kura-kuraina
Ya karbi shahadata
Ya hadani da Maigidana Manzon Allah (saw) a Aljannar Firdausi da sauran musulmi baki daya.
Ameeen.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button