Uncategorized

Riya Da Sunan Neman Addu’a :A Yi Hattara!!! – Dr Sheikh MuhamMuhammad Sani Umar R/Lemo

Riya Da Sunan Neman Addu’a: A Yi Hattara!

Magabata na kwarai na farko, kowane daya daga cikinsu ya kasance mai yawan kaffa-kaffa da ibadarsa, yana boya, ba ya so a sani, tare da hakan yana tsoron ko Allah ya karba ko bai karba ba. 

Amma a yau – ta kafafen sadarwa na sada zumunta (Social Media)- Shaidan ya kawata wa dadama daga cikinmu, mu rika tallata ibadunmu  ga jama’a da sunan muna neman addu’arsu. Dayanmu yakan ce, “Ga mu nan muna Umarah.. 
Ko mun kammala aiki hajji, a ta ya mu da addu’a… Ko yanzu muka kammala tahajjudi, a taya mu da addu’a Allah ya karba…”. Ko ga mu muna karatun alkur’ani… muna neman addu’arku…. Da sauran sakonni irin wadannan. 
Wannan abu ne mai hadarin gaske ga niyyar bawa musulmi. Don haka mu yi hattara!!

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button