Karbar Na-Goro A Ma’aikatun Gwamnati!!!- Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Karbar Na-Goro A Ma’aikatun Gwamnati!!!
Tambaya ?
Assalamu alaikum malam ni ma’aikacin ne da nake aiki a ma’aikatar binciken kudi (state audit), ina cikin team, akwai wasu kudi da ma’aikatar da aka turamu bincike suke bayarwa, kamar haka:
1.kudin Refreshment, maimakon duk rana su kawo mana abinci, sai duk wata sai su bamu dukiya har mu qare aikinmu.
2.kudin sallama. Idan muka kammala sai ma’aikatar ta bamu kudin a matsayin sallamar bakinta.
3. Wasu kudin da ban san ta ina suke fitowa ba, sai dai kawai team leader namu ya kira ni ya bani, dama kuma ko wadancan nau’i 2 da na fada, kirana kawai yake, ya bani abinda zai bani, ba tare da na san a hannun wa ya mso ba, nawa ya amso, ko makamancin haka.
4.Akwai wadanda na san wani mai karin kudi ne ya bayar don a bar shi da karin, suma idan naga sanda ya bayar zai bani, wani wanda ban san sunyi shirinsu ba ba zai ba ni ba.
5. Akwai wadansu mutane da shekarunsu sun kai su aje aiki, ko wasu masu qarin kudi ko ma wasu ghost workers ne babu su wasu ke cin kudin, sai idan nazo rubutu report sai yace kada nayi musu query ya sanda su.
6. Akwai wadanda ake riqe albashin su idan basu zo sukayi verification ba, tanan ne ake, idan mutum yazo sai ayi clearing nashi a bashi salary dinshi, idan bai zo ba ghost workers ne, wani ne ke cin kudin shi, sai a dinga rabe wannan albashin kafin a rubuta report a debe shi a payroll.
7. Shin ya matsayin daukar mataki akan mai qari da yawa kamar mai karin step 7 ko 6 a kyale mai 1?
8. Ko alfarma na shiga ta wannan aikin don kawai sanayya, amma ka dauki mataki ga wanda baka sani ba?
Amsa
Wa alaikum assalam
1. ina muku wasici da tsoran Allah a duk aikin da kuke yi.
2. Duk kudin da kuka San ba halal ba ne ku nisance su, hakan Shi zai sa Allah ya muku albarka a rayuwarku.
3. Bai halatta ma’aikacin gwamnati ya amshi kowanne irin lada ba akan aikinsa da yake amsar albashi akai ba, saboda Fadin Annabi S.a.w. (Duk Wanda muka ba Shi aiki kuma muka ba Shi lada akan haka, to duk abin da ya amsa bayan haka ya zama haram ) kamar yadda Abu Dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (2943).
4. Amsar kudin-goro a wajan masu laifi da niyyar suturta su yana daga ha’inci da kuma rashawar da Allah ya tsinewa mai amsarta, kamar yadda hadisin Tirmizi mai lamba ta: (1336) ya nuna Hakan.
5. Duk wanda ya kiyaye Allah, tabbas zai kiyaye shi, wanda ya keta dokokinsa zai same shi a Madakata, tsarkake abinci na daga cikin hanyoyin karbar addua.
6. Kudin gwamnati haķki ne na jama’ar kasa, taimakawa wani ya ci ba bisa ka’ida ba magudi ne da zai sa su tsaya da shi ranar Alkiyama a gaban Allah .
7.Zunubi Shi ne abin da ka yi amma yake maka yawo a rai kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai.
8. Duk kyautar da aka yiwa ma’aikaici saboda kujerarsa, idan ya amsa ya ci haramun, wannan yasa Annabi S.A.W. ya fusata ya kuma yi kakkausar magana ga IBNU AL-LUTBIYYA lokacin da ya aike Shi amso zakka Amma kuma aka ba Shi kyauta ya amsa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a Sahihinsa.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
12/02/2017
Allah kasa mu dace ku kiyaye Harkukinmu na Yau da Kullum amen