Uncategorized

Gwamnati da ‘Yan kasa: sai An Hada karfi Da Karfe -Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Advertisment

Gwamnati  Da ‘Yan kasa:Sai An Hada karfi da Karfe:

Duk Yadda daula take da karfin tattalin Arziki da wadatar ma’adani,idan har ana son wannan kasa ta ci-gaba wajen ayyukan raya kasa da gina al’ummarta dole ne jama’ar kasa sai sun taimaka mata;kowa daidai gwargwadon abin da Allah ya hore masa,wani da iliminsa ,wani da karfinsa,wani da dukiyarsa ,kowa da  abin zai iya ,to sai ka ga wannan kasa ta ci-gaba,rayuwar al’ummarta ta yi kyau.

Dubi sarkil zul-kurnaini, duk da abin da Allah ya bashi na karfin mulki, ya hore masa na duk wani abin da mai mulki yake bukata don gudanar da mulkinsa ,amma duk  da haka ,lokacin da wadannan kabilu masu makotaka da kabilun Yajuju da Majuju suka nemi agajinsa da ya gina musu ganuwa tsakaninsu da Yajuju da Majuju,sai da ya nemi su taimaka masa da karfinsu don ya yi musu wannan aiki.

Ga abin da Allah ya fada mana ya gudana tsakaninsu :
(suka ce ,”Ya zul-karnaini! lallai Yajuju da Majuju masu barna ne a bayan kasa,shin mu ba ka wani lada ka gina ganuwa tsakaninmu da su.” sai yace ,”Abin da ubangijina ya ba ni ya fi mini alheri ,amma ku taimaka min da karfin don in sanya muku ganuwa ta kankare tsakaninku da su.” [Al-kahfi,94-95].


Allah Akbar kaji manya masu imani wadanda suke biyayya ga Allah da ka’idojin mulki ,Allah ya bamu shuwagabani masu imani.


Dan Allah kayi share zuwa ga abokanan arziki domin ka samu mai yadaa alheri a al’ummarka/ki

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button