Uncategorized
Fatawar Rabon Gadon (100) – Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Advertisment
Fatawar Rabon Gado (100)
Tambaya?
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu, tambaya ita ce yaya za’a raba gadon budurwa wacce ba tayi aure ba, ba uwa da uba sai Yan’uwa da uwansu daya, maza 3 da mata 3, sai kuma wanda ubansu 1, mata 4, da maza 3? Dan Allah malam a taimaka bukatar hakan ya taso ne.
Amsa
Wa alaikum assalam
Za’a raba abin da ta bari gida uku: a bawa ‘yan’uwan da suka hada uwa kawai kashi daya, su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da mace, ragowar kashi biyun kuma sai a bawa ‘yan’uba su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
22/2/2017
Dr Jamilu Zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com