Nigeria: Ana nuna wariya a yaki da cin hanci – Sani
senator shehu sani Daga kaduna |
Shugaban kwamitin majalisar dattawan Nigeria da ya binciki zargin karkata kudaden da aka ware domin kula da ‘yan gudun hijirar Boko Haram ya ce gwamnatin shugaba Buhari na nuna wariya wajen yaki da cin hanci.
Senata Shehu Sani na mayar da martani ne ga wasikar da shugaban kasar ya aike wa majalisar ranar Talata inda a ciki shugaban ya ce ba zai kori sakataren gwamnatin kasar ba kamar yadda majalisar dattawan kasar ta bukata saboda bai gamsu da hujjojin da suka bayar ba.
”A yaki da cin hanci idan ya kasance talaka ne ko wanda bai da galihu sai a kama shi a hukunta shi; idan kuma mutane ne da ke fadar gwamnati sai a kyalesu” ya ce a cikin wata hira da BBC.
Senata Sani da ya ce akwai kura-kurai a cikin wasikar da shugaban ya aiko wadda ta wanke sakataren gwamnatin daga zargin da kwamitin ya yi masa; yana mai nuna shakku ga sahihancinta.
Majalisar dai ta samu wasikar ne a daidai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ke hutun makonni biyu a Burtaniya kuma ya mika ragwamar mulkin kasar ga mataimankinsa.
Abin da wasikar ta kunsa
A cikin wannan wasikar wadda shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya karanta, Shugaba Buhari ya ce shi bai yi aiki da shawarwarin rahoton ba, saboda mutum uku daga cikin mambobin kwamitin ne suka saka hannu, yayin da mutum tara basu saka hannu ba.
Wasikar ta kara da cewar kwamitin bai bai wa Babachir Lawan damar kare kansa ba, kuma kamfanin da ake zargin na Babachir ne shi ma bai samu damar kare kansa ba.
Amma Sanata Shehu Sani, wanda ya shugabanci kwamitin da ya gudanar da binciken, ya kalubalanci wasikar inda ya ce duk abin da ta kunsa ‘karairayi ne’.
Ya yi zargin cewar ba a yakar cin hanci da rashawa a bangaren zartarwa yadda ake yi a bangaren shari’a.
Kawo yanzu gwamnatin ba ta ce komai ba game da zargin da Sanatan, wanda dan jam’iyyar APC mai mulki ne ya yi.
A watan da ya gabata ne wani rahoto da ‘yan majalisar suka fitar ya zargi Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a karbar kwangilar “cire ciyawa” a sansanin ‘yan gudun hijirar, inda suka karbi makudan kudade ba tare da yin aikin da ya kamata ba.
Baya ga haka, ‘yan majalisar sun yi zargin cewa Babachir Lawan ya sabawa ka’idojin aiki saboda ci gaba da zamansa shugaban kamfanin duk da cewa an nada shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
sources bbchausa
senator shehu sani |