Uncategorized

NASIHA A CIKIN MUTANE ,TOZARTAWA NE !! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

NASIHA A CIKIN MUTANE, TOZARTAWA NE ! ! !

Tambaya:
Aslm alkm. Dan Allah meye hukuncin wanda idn yaga anyi kuskure yake toxarta mutum a cikin jama’a? Shugaba ne na mkrnt yake jan jam’i rana daya dalibi yaja da aka idar da sallah sai aka parayiwa dalibin toxarta a gaban dalibai maxa da mata kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kirashi gepe an masa pada da karin haske ko a hadasu iya maxa ayi musu xaipi. Meye hukuncin haka?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Yiwa mutum Nasiha a cikin mutane bai dace ba, kuma hanya ce da za ta hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa nasihar yana da tsananin iklasi ba, Annabi s.a.w. yana cewa: “Wanda ya suturta musulmi Allah zai suturta shi”, kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2074.
Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button