Uncategorized
Fatawar Rabon Gado (94)- Dr jamilu Yusuf Zarewa
Advertisment
Fatawar Rabon Gado (94)
Assalamu Alaikum da fatan mallam yana Qoshin lafiya
Dan Allah mallam ya za’ayi rabon gadon matan da ta rasu tabar mijinta da yarinya 1 da kanne maza 2 da mave 1 wanda suka hada uwa daya uba daya, da kuma namiji 1 da mace 1 wanda suka hada uba daya ,da kuma namiji 1 da mata 2 wanda suka hada da uwa daya dasu.
Nagode Allah ya kara mana ilimi mai albarka
Amsa
wa’alaikum assalam za’a raba abin da ta bari gida hudu,miji za’a bashi daya ,ita ‘yar za’a bata biyu,zai rage saura daya shi za’a bawa yan’uwanta da suka hada uwa da uba su raba.Namiji zai dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
Amsawaa
Dr jamilu Yusuf Zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com