Uncategorized

FATAWAR RABON GADO 93 DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO 93*

*_Tambaya:_*
Salam Alaikum, Allah ya karama malam lafiya amin. Ina da tanbaya akan gado. Malam mahaifiyace ta rasu tabar mijinta da mahaifiyarta, da kaninta da yarta sannan da yara takwas maza biyar mata uku. Ya rabon gadonta zai kasance. Nagode. 

*_Amsa:_*
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ta bari gida sha biyu: a bawa mahaifiyarta kashi biyu (Sudus), sai a bawa mijinta kashi uku (Rubu’i), Ragowar kashi bakwan sai a bawa ‘ya’yanta su raba duk namiji ya dau rabon mata biyu. 

‘Yan’uwa ba sa gado mutukar a ‘ya’yan mamata akwai namiji.

Allah ne mafi sani. 

✍? Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
18/1/2017

posted  Abubakar Rabi’u

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button