An Bude Katafaren Masallacin Da Sanata Kabiru Gaya Ya Gina A Abuja a cikin (Hotuna)
An Bude Katafaren Masallacin Da Sanata Kabiru Gaya Ya Gina A Abuja
Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya gabatar da wa’azi kafin zuwan liman, inda Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya gabatar da khuduba da Sallar Juma’a.
Gwamna jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bude katafaren masallacin juma’a wanda Mai Girma Sanata Kabiru Gaya ya gina a unguwar Wuse Zone 6 dake babban birnin tarayya Abuja.
Sauran manyan baki sun hada da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki wanda Sanata Yarima Bakura ya wakilta da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu da Mai Girma Sanata Barau Jibrin da yan majalisar dattijai da ta wakilai da Alhaji Dahiru Mangal da kuma sauran alumma Musulmi.
A jawabin sa Sanata Kabiru Gaya ya yi godiya ga wadanda suka taimaka wajen gina wannan masallacin juma’a wanda shine na farko a unguwar ta Wuse Zone 6. Inda ya yi kira ga alummar Musulmai da su cigaba da taimakawa dan gudanar da masallacin da sauran masallatai.
Allah ya sanya albarka. Amin.
posted by Abubakar Rabi’u