Uncategorized

TARIHIN RUWAN ZAMZAM MAI ALBARKA |SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

RUWAN ZAMZAM MAI ALBARKA

Tarihin wannan ruwa, kamar yadda yazo a cikin
Sahihul Bukhari, Lokacin da Annabi Ibrahim (AS) ya
ajiye matarsa,da dansa, a wajan, Mala’ika Jibrilu, ya
buga wajan da duddugansa, sakamakon haka aka
sami ruwan Zamzam,
Wannan ruwa dashi aka wanke zuciyar Annabi
saw, a lokacin yana dan shekara hudu, a wajan
Halimatus- Sadiya, da kuma lokacin tafiya Isra’i
Manzon Allah saw yace: Ruwan zamzam, (zaa sami
biyan bukata da niyar ) da aka sha. Sahihu ibn
Majah.
idan mutum zai sha ruwan zamzam yasha da niyya
mai kyau, kuma yayi addu’a ta gari, kamar yadda
magabata sukeyi,
A wani hadisin yace : Ruwan mai albarka ne,
abincin mai cine, kuma ruwan mai sha ne. Muslum
2473
A wata Riwayar, Ruwa ne mai albarka, abincin mai
ci, waraka daga rashin lafiya, Assunanul kubra
Baihakiy, ajamiu- Sahih 2435
A wata, riwayar, Mafi alkhairin ruwa a bayan kasa
shine ruwan zamzam. Sahihut-targib wat-tahib.
Nana Aishah ta kasance, tana guzirin ruwan zamzam a cikin kwalbah,
kuma tace: Manzon Allah saw, yana guzirin ruwan
zamzam, a cikin salka, yana zubawa, marasa lafiya,
yana shayar dasu, Sahihut- tirmiziy.
Mal,Ibnul- Qayyim yace, yaga abin al’ajabi gamai da
ruwan zamzam, daya gamu da rashin lafiya a maccah lokacin babu likita sai ya gwada amfani da
ruwan zamzam, yana tofa suratul fatihah a ciki, ya
sha ya sami lafiya. Zadul- maad
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button