Uncategorized

TA’ADDANCIN ‘YAN SHI’AH A KASAR SYRIA DA TAIMAKON KASAR RASHA DA IRAN |DR SANI UMAR MUHAMMAD R/LEMO

TA’ADDANCIN ‘YAN SHI’AH A KASAR SYRIA DA TAIMAKON KASAR RASHA DA IRAN

Daga Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Ilmi yaka cewa;
A cikin ‘yan kwanakinnan na abubuwa da suke faruwa na kisan kiyashi da abubuwa na tashin hankali da bakin ciki ga ‘yan uwanmu musulmi kuma ahlussunnah wadanda suke a garin Halab kasar Syria.
Garin Halab wanda turawa suke cewa Aleppo, Halab yana daya daga cikin dadadden garuruwa a duniya, a tarihin kafuwar duniya yana daya daga cikin dadadden garuruwa domin garin Halab ya riga garin Ruma da wajen shekara dubu uku (3000), saboda haka garine dadadde ba wai na yanzu ba.
Kuma yana daya daga cikin garuruwa wanda suke kunshe da kayan tarihi masu dumbin yawa kwarai dagaske, shiyasa zakaga cewa hatta a cikin abubuwa da ake ambato na tarihi akace Annabi Ibrahim (AS) yabi ta garin lokacin da zai tafi Palasdine yayin da ya baro yankinsa na cikin Iraqi ko arewacin Iraqi zai shiga Palasdine yabi ta Halab.
Abinda yake faruwa a Halab; Halab dinnan lokacin da suka shiga zanga-zanga ba ‘yan #ISIS a Halab, ba wani ‘dan #Tadribu_Daula a Halab ko daya babu sojojinsu, inda suke da karfi shine Raqqah, Raqqah dinnan har yanzu sojojin basu kai musu hari ba.
Wadanda aka sasu cikin kwandon ‘yan ta’adda sune ‘yan #Jabhatunnusrah wanda suma sunce ba ruwansu da #Alqaidah su yanzu ‘yan kasa ne ‘yan Syria ne kamar kowa, yanzu suna neman ‘yan cinsu ne don haka ba wani umarni da zasu karba daga Alqa’idah ta duniya, sunyi wannan har suka canza sunansu daga Jabhatunnusrah suka koma #Jabhatu_Fathu_AlSham, to guda nawane a cikin Halab din da yanzu ake rugurguzawa yanzu gaba gaba daya?
A halab din da ake rugurguzawa akwai mazauna garin sunfi su dubu dari biyu (250,000+), to wadanda suke ‘yan Jabhatunnusrah a garin dudu basu wuce su dari biyu ba (200).
Sauran kuma mayaka da ake dasu wadanda su basa cikin ‘yan ta’adda; iyaka dai kawai tunda zasu daga tuta na musulunci kasan dole turawa suce ‘yan ta’adda ne, indai zaka saka “la’ilaha illalLah” a jikin tutarka to kawai ka zama ‘dan ta’adda a wajensu duk da baka kashe kowa nasu, bakayi musu barazana ba.
Akwai ‘yan #Jaisul_Islam akwai ‘yan #Ahraru_Sham d.s wanda duk suna cikin Halab, gaba daya basu kai dubu goma ba (10,000), ana maganar mazauna garin gaba dayansu dubu dari biyu da hamsin, amma ka duba kaga yanda gaba dayan garin an rusashi, babu abinda ya saura a garin gaba daya an rusa garin, an kashe mutane ba’asan adadinsu ba, yanzu lissafi baza’a iya sanin lissafin nawa aka kashe ba tsakanin maza yara da mata, an rusa duk wata kasuwa da ka sani a garin Halab, an rusa duk wata asibiti da aka sani a garin, an rusa duk wata makaranta da duk wani masallaci.
Kwanaki cewa suke mayakan ma wanda suke ciki dubu daya ne, wannan wakilin majalisar dinkin duniya kenan, abinda yake fada cewa akwai mayaka dubu daya wanda suke cewa ‘yan ta’adda ne su fita, cikin dubu dari biyu da hamsin kana maganar dubu daya, saboda dubu daya ka rusa gaba daya garin ka kashe duk mutanen garin, babu wani ‘dan ta’adda da zaiyi wannan abin, abinda sukayi yafi na ‘yan ta’addan
To tunda aka gayyato #Rasha tazo da makamanta wasu ma anan Halab ta fara gwadasu, akwai makaman da bata taba amfani dasu ba sai a garin, ta kawo manyan jiragenta na yaki na ruwa tazo ta girke wanda daga nan jirage zasu dinga tashi, #Iran ta bata #base (sansani) inda nan ma zata rike airport sune, inda nan ma zasu dinga tada jirage suna kai hare-hare, a rana daya sai sukai #attack sama da 200 a rana daya, tun sanda suka fara kai attack masu fadar albarkacin baki suke cewa in sunkai attack dari to baifi sau daya zasu kaiwa ‘yan ISIS ba.
Abinda zaisa ku kara fahimtar wannan ana cikin wannan gumurzun na Halab suna mutsuts-tsukar ‘yan Halab maza da mata da yara suna musu ruwan bama-bamai sama da kasa, ana cikin haka ‘yan ISIS suka karbi #Tadmur, Tadmur dinnan babban garine a kasar Syria, babban garine kuma na tarihi, amma sukazo sukayi fada suka kori sojojin Bashar Al’asad Syria suka kwace garin suka kafa tutarsu.
Kuma ku kunce kuna yaki da ‘yan ta’adda kuma ga (ISIS) wadanda duk duniya tayi ittifaqin cewa sune ‘yan ta’adda, don menene kuka barsu kukazo nan (Halab) kuna mutsuts-tsukar gurin da ana maganar akwai ‘yan Jabhatunnusrah mutum 200 kacal? To wannan shi zai nuna maka cewa basa son yanzu suce zasuyi fada da ‘yan ISIS saboda so suke abinda shi Bashar Al’asad yakeso ya zama, ya zama yanzu ya gama da dukkan wani wanda yakeso ya masa tawaye, ya zama babu saura da suka rage sai ‘yan ISIS sai shi.
Insha Allahu zan cigaba da gabatar da rubutu kashe biyu na Dr Sani Rijiyar Ilmi
Allah (T) muke roko ya rushe ta’addancin shi’ah a duniya
Yaa Allah Ka kwace duk wani karfi da ‘yan ta’addan shi’ah suke gadara dashi
Yaa Allah Ka wautar da kwakwalen ‘yan ta’addan shi’ah su koma hallaka junansu
Yaa Allah AlHayyu AlQayyum Ka kyale ‘yan ta’addan shi’ah da wayonsu da dabararsu
Yaa Allah Ka cire taimakonKa akan ‘Yan ta’addan shi’ah
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button