Uncategorized
MAGANIN CUTAR SIKILA ! ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
MAGANIN CUTAR SIKILA ! ! !
Tambaya :
Malam muna da wata yarinya da take fama da cutar sikila, to shi ne mu ka je wajan mai magani , sai ya ce mana mu samu naman kunkuru da jininsa, idan muka yi amfani da shi za ta samu sauki, shi ne muke so mu ji halaccin hakan a wajan malamai ?

Amsa :
To ‘yar’uwa Allah madaukakin sarki, bai saukar da cuta ba, saida ya saukar da maganinta, sannan kunkuru yana daga cikin namun da ya halatta a ci, saboda haka idan ya tabbata a likitance cewa namansa yana maganin cutar skila, to za ku iya

amfani da shi, amma ba za ku iya amfani da jininsa da ya kwarara ba, saboda Allah ya haramta amfani da jinin da ya kwarara,
kamar yadda hakan ya zo a suratu Al’an’am aya ta :145 , amma abin da ya ragu na jini a cikin namansa, wannan ya halatta ayi amfani da shi.
Masana likitanci suna cewa, sikila wani rauni ne a cikin jini, don haka ba cuta ba ce, balle har ta warke,
amma akwai magungunan da suke rage mata kaifi, daga ciki akwai OSPEN da FOLIC ACID.
Allah ne mafi sani.
Allah ne mafi sani.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com