FATAWAR RABON GADO VO.1
RABON GADO (1)
Tambaya : salam. malam, mutum ne ya mutu yabar kudi
#200,000. yana da mahaifi da ‘ya’ya maza 3, mace daya, da kuma matar aure daya, ya gadonsu zai kasance?
Amsa :
To da farko dai za’a
kasa gida 24 ne, sai a bawa matar auren kasha uku daga ciki “thumuni” wato 25000 kenan, sai kuma a bawa mahaifinsa kashi hudu daga ciki, sudusi” 33333.3333, kenan, ragowar kuma wato 141666.667, sai a rabawa yaran gida bakwai, a bawa kowanne namiji kashi biyu wato 40476, macen kuma a bata : 20238.0953.
Allah ya ba mu dacewa.
RABON GADO (2)
Tambaya :
Malam mace ce tamutu ta bar babarta da ‘yan’uwanta shakikai maza, da ‘yan’uwanta wadanda suka hada uba daya, da baffaninta, don Allah yaya za’a raba gadon ?
Amsa :
To dan’uwa za’a kasa dukiyar gida shida, inda za’a baiwa uwa kashi daya, ragowar kashi biyar din kuma sai a baiwa ‘yan’uwa shakikai, baffani da ‘yan’uwan da akahada uba daya da su ba sa cin gado,mutukar akwai ‘yan’uwa shakikai maza .
Allah ne mafi
sani.
RABON GADO (3)Tambaya : Assalamu alaikum barka
da iwar haka, ina da tambayoyi (2) Matata ta mutu ta bar ni da yaro da yara mata biyu, babanta, babarta da ‘yan’uwanta maza 3 da mata 2, don Allah yaya rabon gadon abin da tabari yake, sannan kayanta nasawa da kayan daki yana daga ciki abinda za’a rabawa magada. Allah ya saka da alkhairi.
Amsa :
To malam ina rokon Allah ya jikanta, za’a raba dukiyar gida sha biyu, a baka kashi uku a ciki, sai a bawa babarta kashi biyu, babanta shi ma
kashi biyu, ragowar kashi biyar din sai a rabawa ‘ya’yanta, za su raba abin da aka ba su kasha hudu. Namijin ya dauki kashi biyu kowacce
mace ta dauki kashi daya, ‘yan’uwanta ba za’a ba su komai ba, saboda yaranta sun ka tange su. Dukkan abin da ta bari za’a raba da shi, har
kayan dakinta, tun da yana daga cikin abin da ta mallaka.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
RABON GADO (4)Tambaya: Assalamu alaikum,
malam wata matsala ce ta taso mun. Miji na ne
ya rasu. sai aka ce za’ayi rabon gado, ‘ya daya muka haifa,sai ni matar shi,sai kanin shi da suke uwa1 uba1,sai yan’uwan shi da suke uba 1,sai mahaifiyar shi wanda ba ta musulunci, mahaifinshi ya rasu. To don Allah yaya rabon yake. ?
Amsa:
To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya yi
masa rahama, za’a raba dukiyar da ya bari gida
takwas, a bawa ‘yarsa kashi hudu (Rabi) , a ba ki kashi daya, (1/8) dan’uwansa shakiki a ba shi ragowar. Mahaifiyarsa ba za’a ba ta komai ba tun da ba ta musulunta ba, saboda kafiri ba ya gadon musulmi, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisi, haka nan yan’uwansa da suke uba daya, ba za’a ba su komai ba tun da akwai kanin sa shakiki..
Allah ne mafi sani.
RABON GADO (5)Tambaya : DR. Mutum ya mutu
yabar matarsa 1, da da namiji 1, da ‘ya’ya’
mata 4, da uwa da uba, da kuma yan’uwansa da suke uwa daya uba daya.ya rabon gadon zai kasance. Allah ya kara basira
Amsa :
To dan uwa za’a raba dukiyar gida 24, sai a bawamatarsa kashi uku dga ciki, (1/8), za’a bawa uwa kashi hudu (1/6) haka shi ma uba za’a ba shi, ragowar kashi sha ukun sai a bawa ‘ya’yansa su raba, namiji zai dauki kason mace biyu. ‘Yan’uwansa ba za’a ba su komai ba, saboda akwai ‘yaya.
Allah ne mafi sani
RABON GADO (6)Tambaya : Assalamu alaikum malam ina da tambaya Mutum ya mutu sai ya bar yayyi 2 , maza da yayyi mata wadanda suke uba 1, da kuma mahaifiyar sa ya za a raba musu gado ?
Amsa:
Za’a raba dukiyar gida
shida, a bawa uwa kashi daya, ragowar kasha biyar din a bawa yan’uwa su raba. Namiji ya dauki rabon mata biyu.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
RABON GADO (7)Tambaya : Mutun ne ya mutu
ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa da kannansa wadanda suke uwa 1 uba1 da wadanda suke uba 1, malam yaya za’a raba dukiyar da aka bar musu ?.
Amsa :
To dan’uwa za’a raba dukiyar gida shida, a bawa uwa kashi daya, sai a bawa uba ragowar kashi biyar din, kanne ba su da komai saboda uba ya katange su.
Allah ne mafi sani .
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
RABON GADO (8)Tambaya : Malam mutum ne
ya bar kakansa da babarsa da dan’uwansa da suka hada da uba, yaya za’a raba gadon ?
Amsa :
To dan’uwa za’a kasa dukiyar gida uku, a baiwa babarsa daya bisa ukun abin da ya bari, sai a baiwa kakansa daya bisa uku, dan’uwansa shi ma sai a a ba shi ragowar daya bisa ukun.
Allah ne mafi sani .
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
RABON GADO (9)Tambaya: Wato malam
mahaifinmu su ukune awaje mahaifinsu ,mahaifin namu da kuma kannensa mata guda biyu, kaga su uku kenan, to shi maihaifinmu sai
Allah yayi masa rasuwa shekaru biyar da suka wuce, ya bar mahaifinsa da kannan nan nasa mata guda biyu, to kwanannan kuma wata uku da suka wuce sai Allah ya yiwa shi wannan kaka namu rasuwa kafin yarasu sai yace a bamu wani gida saboda mahaifinmu bai gaje shi ba, muma kuma ba za mu gaje shi ba, to amma kuma wani malami yace min za mu gaji kakannamu saboda mahaifinmu kadai dansa namiji, sannan malam kakan na mu ya bar mata guda daya, malam zuciyata ta kasa nutsuwa ya abin yake, nagode Allah ya karama ilmi da takawa.
Amsa:
To dan’uwa ina rokon Allah ya
amsa addu’arka, tabbas kuna da gadonsa, saboda ‘ya’yan mamacin da matarsa, ba za su cinye dukkan dukiyar ba, sannan abin da ya ba ku yana raye ba zai hana ku cin gado ba, don haka, za’a raba dukiyar gida 24 a bawa kannen mahaifinku mata gida 16, matarsa kashi uku, ku kuma a baku ragowar.
Allah ne mafi sani.
DR.JAMILU YUSUF ZAREWA
FATAWAR RABON GADO (10)Tambaya:
Assalamu alaikum Mal. Jameelu ina da tamabaya akan sha’anin rabon gado. Tambayar ita ce kamar haka: mutum ne ya mutu yabar ‘ya’ya mata biyu kadai, sai kaninsa wanda suke uba daya, amma ba su hada uwa ba, ya rabon gadonsu zai kasance, shi yana da gado ko kuwa?
Amsa :
To dan’uwa za’a raba dukiyar gida shida, a bawa ‘ya’ya matan kashi hudu, shi kuma kanin na sa sai a ba shi ragowar.
Allah ne ma fi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
RABON GADO (11)GADON MATA-MAZA ! !
Tambaya : Assalamu alaikum, idan mutum ya mutu ya bar
mata-maza da ‘yan’uwa, yaya rabon gadon zai kasance ?
Amsa :
To dan’uwa mata- maza shi ne wanda yake da al’aurar mace da ta namiji, kuma ya kasu kashi biyu : 1. Akwai mara
rikitarwa, wato wanda aka gane inda ya fi karfi, kamar ya zama yana haila, kaga za’a riskar da shi da mace wajan rabon gado, ko ya zama
yana fitsari ta al’aurar namiji, to wannan hukuncinsa hukuncin namiji a wajan rabon gado
haka nan idan ya zama yana da gemu da gashin baki. 2. Mai rikitarwa, wannan shi ne wanda aka
kasa gane inda ya fi karfi, kamar ya zama yana fitsari ta ala’aura biyu, kuma ba wanda yafi fitowa da karfi ko da yawa a cikinsu, ko kuma
ya zama yana da gemu, kuma yana haila. Idan har mata maza ya balaga ba’a gane inda yafi karfi ba, to za’a ba shi rabin gadon mace ne, da rabin gadon namiji. Duba : Attahkikat
almardhiyya fi-mabahithil-fardhi yya shafi na 206.
Allah ne mafi sani
FATAWAR RABON GADO (12)Tambaya :
Assalamualaikum. Malam tamabaya che kamar
haka : mutun ne ya mutu ya bar uba da uwar
uwa da yaya maza da mata yaya rabon zai kasanche Allah kara basira.
Amsa :
To dan’uwa
za’a raba gida shida, a bawa uba kashi daya, sai Uwar uwa kashi daya, sai a bawa ‘ya’yan ragowar, su raba, na miji ya dau rabon mata biyu Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FA
TAWAR RABON GADO (13)Tambaya :
Assalamu Alaikum Warahmatullah. Malam mutum ne ya rasu, ya bar mahaifiyarsa da mata biyu da kuma ‘ya’ya mata da maza. Ya rabon
gadonsa zai kasance? Allah ya saka maka da alheri malam.
Amsa:
To dan’uwa za’a raba
dukiyar gida 24, a bawa mahafiyarsa kashi 4, sai abawa matansa kashi 3 su raba, sai a baiwa ‘ya’yansa ragowar., su raba a tsakaninsu, duk namiji zai dauki gadon mata biyu.
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FATAWAR RABON GADO (14)Tambaya:
Assalamu alaikum- Inai wa Malam (Dr) fatan alheri bayan haka, Ina neman fatawa
kan matsalar GADO. Wani mutun ne ya rasu ya bar MATA 3, da ya‘yamaza 16 da kuma mata 11. Tambayar itace yaya rabon gadon zai kasance (wato kashi nawa za‘a raba)
Amsa
To dan’uwa za’a raba abin da ya bari
gida takwas, sai a bawa matansa kashi daya su raba a tsakaninsu, ragowar bakwan kuma sai a bawa ‘ya’yansa su rabe, duk namiji zai dauki rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FATAWAR RABON GADO (15)Tambaya:
Malam watace ta mutu bata da ya’ya amma tanada miji da uwa da yan’uwa shakikai da li ummai da li abbai ya rabon zai zama ?
Amsa:
To dan’uwa za’a raba Gida 6, sai a bawa Uwa kashi daya, miji kuma a ba shi kashi uku, rogowar kuma sai a bawa ‘yan’uwa shakikai da Li’ummai su raba a tsakaninsu, za su raba daidai babu banbanci tsakanin mace da namiji.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FATAWAR RABON GADO (16)Tambaya:
Assalamu Alaikum Allah ya karawa Dr lafiya da Imani Amin, malam dan Allah ‘ya’ya rabon gadon matan da ta rasu ta bar yaya biyu mata amma duk ‘ya’yan mazan sun mutu kafin ita. Amma su ‘ya’yan mazan suna da ‘ya’ya. Idan ‘ya’yan matan sun gaji 2/3 sauran1/3 jikokin ‘ya’yan da basu gaje ta bane za su raba koko har da yayan wadanda suka gaji 2/3 ?
Amsa:
Wa alaikum as salam, To dan’uwa Za’a raba dukiyar gıda uku, kamar yadda ka fada sai a bawa ‘ya’yan nata mata kashi biyu, ragowar sai a bawa jikokinta na bangaren ‘ya’yanta maza, jikoki ta bangaren mace ba sa gado.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FATAWAR RABON GADO (17)Tambaya: Malam mutun ne ya rasu yabar mahaifiya da ‘yan uwa li’abbai da li’ummai, to li’abban suna da gadonsa?
Amsa:
Idan ya zama haka, Za’a raba
dukiyar gida shida, a bawa uwa kashi daya (sudus), sai a bawa ‘yan’uwa li’ummai kashi
biyu(thuluth), ragowar ukun sai a bawa ‘yan’uwa li’abbai, ‘yan’uwa Li’ummai Za su raba daidai, babu banbanci tsakanin namiji da
mace, kamar yadda aya ta: 12 a suratunnisa’i ta tabbatar da haka. Allah mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa
FATAWAR RABON GADO (18)Tambaya: Malam
mutum ya mutu ya bar shaqiqinsa da kanin
matarsa, kanin matar yayi gado, shaqiqin bai gaji komai ba tambaya yaya abun yake ne?
Amsa:
Wannan kam kusukure ne, in har su biyu
kawai aka bari, to shakikin shi ne zai gaji duka dukiyar, kanin matar ba shi da komai,
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu yusuf zarewa