FA’IDOJIN RUWAN ZAMZAM 36 | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO
FA’IDOJIN RUWAN ZAMZAM 36
1 ZAMZAM, MALAIKA JIBRILU, YA TONA SHI.
2 ANNABI ISMAILA YA FARA SHAN ZAMZAM.
3 ZAMZAM SHINE ASALIN KAFUWAR BIRNIN MACCA
4 DA ZAMZAM AKA WANKE ZUCIYAR ANNABI SAW.
5 BABU RUWAN DA YA FISHI DARAJA, A DORAN KASA. 6 ANNABI SAW YA SHA RUWAN ZAMZAM.
7 ANNABI SAW YA ZUBASHI A JIKINSA.
8 ANNABI SAW YAYI GUZIRIN SA ZUWA MADINA.
9 ANNABI SAW YACE ,RUWAN ZAMZAM ZAKA SAMI
BUKATAR DA KASHA SHI, SABODA ITA.
10 NANA AISHATU RA, TANA GUZIRIN ZAMZAM. 11 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM, MALAMAI
SUKAYI SABANI, GAMAI DA WANKA DA SHI, DA
ALWALA DA TSARKI DA WANKE NAJASA.
12 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM MALAMAI
SUKAYI SABANI, DA SHI DA RUWAN KAUSAR A WANNE
YAFI? 13 MAL IBN HABIB BAMALIKAI, YACE ANSO GA WANDA
YAYI HAJJI, YA YAWAITA SHAN ZAMZAM, SABODA
SAMUN ALBARKA, YAYI ALWALA YAYI WANKA.
14 SHAIK ALBANIY YACE, YA KAMATA ALHAJI, YAYI
GUZURI DA ZAMZAM, DOMIN NEMAN ALBARKA,DOMIN
ANNABI YAYI GUZIRIN SA A CIKIN GORA DA SALKA ZUWA MADINA, YANA ZUBAWA MARASA LAFIYA YANA
SHAYAR DA SU.
15 MAL ANNAWAWIY, YACE , MAZAHABARMU KAMAR
TA JAMHURIN MALAMAI, BABU LAIFI AYI WANKA DA
ZAMZAM, KUMA AYI ALWALA.
16 MAL WAHAB IBN MUNABIH YACE: ZAMZAM ABIN SHAN MASU NAGARTA, YANA TSAYAWA A MATSAYIN
ABINCI DA ABIN SHA, KUMA WARAKA DAGA LARURA.
17 MAL KHALIL, A CIKIN MUKTASAR YACE : YANA DAGA
CIKIN ABINDA AKE SO GA ALHAJJI, YA YAWAITA SHAN
ZAMZAM.
18 ACIKIN SHARHIN AN SANHURIY YACE: YANA DAGA CIKIN ABINSO, YAWAITA SHAN ZAMZAM, DA ALWALA,
DA WANKA, DA YAWAITA ADDUA A LOKACIN SHAN
ZAMZAM GA ALHAJI.
19 AL IMAM SHAFII, YACE: MUSTAHABBI NE YAWAITA
SHAN ZAMZAM.
20 MALAMAI SHAFIAWA SUNCE: MUSTAHABBI NE SHAN ZAMZAM, DA YAWAITA SHAN SA, KUMA ANSO MUTUM
YA SHIGA CIKIN INDA RIJIYAR ZAMZAM TAKE, YA KALLI
RUWAN, YA DEBO DA GUGA, YA SHA YA ZUBA AKANSA.
DA FUSKARSA, DA KIRJINSA, KUMA YAYI GUZURI DA
SHI.
21 MAL HASANUL BASARI YACE: IDAN AN SHA RUWAN ZAMZAM AYI ADDUA, YANA CIKIN GURARE 15 DA AKE
SA RAN KARBAR ADDUAR MASU AIKIN HAJJI, SUNE
WAJAN DAWAFI, MULTAZAM, KARKASHIN INDARARO,
CIKIN KAABA, ZAMZAM, KAN SAFA, KAN MARWA,
CIKIN SAAYI, BAYAN MAKAMU IBRAHIM, MUNA, FILIN
ARFA, MUZDALIFAH, JAMRA GUDA BIYU TA FARKO DATA BIYU ANA TSAYAWA AYI ADDUA.
22 ABDULLAH DAN ABBAS RA, IDAN YA SHA ZAMZAM
SAI YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH KA BANI ILMI MAI
AMFANI , DA ARZIKI MAI YALWA, DA WARAKA DAGA
DUKKAN LARURA.
23 ABDULLAH DAN MUBARAK IDAN YA SHA ZAMZAM SAI YA KALLI GABAS YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH
MANZON ALLAH SAW YACE, RUWAN ZAMZAM ZAKA
SAMI BUKATAR DA KASHA SHI SABODA ITA, TO GANI
NA SHA, KA RABANI DA KASHIRWA RANAR
ALKIYAMA.
24 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN ZAZZABI DA MASHASHARA.
25 RUWAN ZAMZAM YANA ZAMA DALILIN KANKARE
ZUNUBI WANDA YASHA DA NIYAR TUBA
26 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN HADDA,
WANDA YAKE SHA DA NIYAR HAKA, KAMAR YADDA AL
IMAM SUYUDIY YAYI YA ROKI ILMIN FIQHU DA HADIS. 27 RUWAN ZAMZAM YAN KARA KARFIN MUTUM WAJAN
MU’AMALA DA IYALI,
28 SHAN ZAMZAM ALAMACE TA IMANI.
29 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN YAWAN JIRI,
30 WANKE FUSKA DA ZAMZAM YANA KARA KARFIN
IDO. 31 SHAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN ZUCIYA.
32 SHAN ZAMZAM YANA TAFIYAR DA YAWAN FIRGICI
DA TSORO.
33 SHAN RUWAN ZAMZAM YANA RAGE GIRMAN KAI.
YANA HORE ZUCIYA.
34 KALLON RUWAN ZAMZAM YANA DA AMFANI. 35 MAL ALBANIY YACE: YA GAMU DA WATA LARURA
WANDA LIKITA YACE SAI ANYI MASA AIKI, AMMA
KAFIN ZUWAN RANAR AIKIN, DA YA DUMFARI SHA
RUWAN ZAMZAM, DA LOKACIN AIKIN YAYI, SAI AKA CE
BABU CUTAR YA WARKE, SILSILA
36 MAL IBNUL QAYYIM YA KAWO A CIKIN LITTAFIN SA. ZADUL MAAD, CEWA: YA GAMU DA LARURA A MACCA
YA RASA LIKITA, SAI YA DEBI RUWAN ZAMZAM YANA
KARANTA FATIHA YASHA, NAN TAKE YA WARKE.
DUBA WANNAN LITTAFIN DOMIN KARIN BAYANI
ﻒﻴﻟﺄﺗ ﻪﻟﻮﻟﺍﻭ ﺶﻫﺪﻟﺍ ﺔﻟﺍﺯﺇ
ﻱﺭﺩﺎﻘﻟﺍ ﺲﻳﺭﺩﺇ ﻦﺑ ﺪﻤﺤﻣ ﺶﻳﻭﺎﺸﻟﺍ ﺮﻴﻫﺯ ﻖﻴﻘﺤﺗ
ﻲﻧﺎﺒﻟﻷﺍ ﺦﻳﺮﺨﺘﺑ
37 AKWAI BINCIKE DA WATA CIBIYA TA KASAR TURE
TAYI AKAN ZAMZAM, DA FA’IDOJINSA A ZAMANANCE,
A DUBA WIKIPEDIA .