Uncategorized
BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!!
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahamatullah, dan Allah inaso a amsa min wannan tambayar:-shin kowata irin rantsuwa ce ake yin mata kaffara kokuwa ba kowace bace ake yiwa kaffara ba ? na gode.
Assalamu alaikum warahamatullah, dan Allah inaso a amsa min wannan tambayar:-shin kowata irin rantsuwa ce ake yin mata kaffara kokuwa ba kowace bace ake yiwa kaffara ba ? na gode.
AMSA:
Wa alaikum assalam, ba kowacce rantsuwa ake yiwa kaffara ba, rantsuwoyi a fiqhun musulunci iri uku ne:
Wa alaikum assalam, ba kowacce rantsuwa ake yiwa kaffara ba, rantsuwoyi a fiqhun musulunci iri uku ne:
1. Rantsuwar da aka yi akan karya, wannan tana iya turbutsa mutum zuwa wuta, ba ta da kaffara sai istigfari, saboda girman zunubinta.
2. Rantsuwar da ta zo baki yayin magana ba tare da nufi ba, wannan Allah ya yi afuwa akanta, kamar yadda ya bayyana a aya ta: 224 a Suratul Bakara. i
3.Rantsuwa akan wani abu da zai zo nan gaba, kamar ya ce : wallahi gobe zan je wuri kaza, in bai je ba, zai yi mata kaffara, kamar yadda aya ta: 89 a suratul Ma’ida ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com