Uncategorized

NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI!!!!|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI   ! ! ! !
Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da fatan malam yana lafiya,
Malam ya halatta namiji yayi kunshi?
Amsa:
Wa alaikum assalam
Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi  s.a.w. ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R.A lokacin da ya musulunta ranar bude Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al’ar’na’u’d ya inganta.
Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la’anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784.                                                                                                                            Yana daga cikin ka’diojin da ya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana sabawa daga al’ada zuwa wata.
Allah ne mafi sani
15/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button