Uncategorized

Maganar Gaskiya AKan Tsotar Al’aura Ga Ma’aurata ( Oral sex) Dr jamilu Yusuf Zarewa

MAGANAR GASKIYA AKAN TSOTSAR AL’AURA GA MA’AURATA ( Oral sex) :
By Anas Assalafy Fagge :

An tambayi dan uwa Dr Jamilu Zarewa dangane da halaccin tsotsar al’aura ga ma’aurata kuma Dr, Allah ya saka masa da alheri ya bada fatawar halacci, duba da dalilai da suke nuni akan haka.
Bayan yaduwar wannan fatawa a kafar sadarwa ta zamani ( social media) se daya daga cikin ‘yan uwa malamai yayi rubutu akan wannan fatawar ta Dr Zarewa kuskure ce, shima ya kawo dalilansa,
Lallai wannan shine ilimi kuma haka manhajin mu yake.
Amma maganar gaskiya itace fatawar halaccin, kamar yadda Dr Zarewa yayi fatawa.
Ga kadan daga cikin dalilai akan halaccin hakan ( Oral sex) :

1- Imamaul-bahuty ya fada a littafin “Alkashf” 5/209:
” alkali Abu ya’ala alhanbaly yace : ” sunbantar farjin mace ya halatta kafin jima’i, an karhanta bayan gama jima’i “.

2- imamul-mardawy ya naqalto a cikin Al-insaaf 8/33 yace : daga A’da’ yace : ” za’a iya lasar farjin ko sumbantarsa.

3- wannan itace fatawar Alfatuhy ya bayar a cikin Muntahal-iradaat 4/55.

4- Imamu Alqurduby ya naqalto a cikin Tafsirin sa 12/231 :
” mutane sunyi sabani wajen halaccin mutum yaga al’aurar Matar sa zuwa magana biyu : a ciki yake cewa ” malam Asbag daga cikin malaman mu yace: ” ya halatta ga Miji ya lashi (farjin) Matar sa da harshe”.

5- Imam Assuyudy a cikin “shaqa’iqul-utrujj” shafi na 107:
” an tambayi Asbag : shin Miji ze iya kallar farjin Matar sa yayin jima’i? Se yace:
” eh, ze iya lasa, yana nufin da harshen sa, babu laifi.
Daga cikin malaman wannan zamanin wadanda suka tafi akan halaccin hakan akwai:

* As-sheikh Aliyu jum’ah
* ustazu Aldoktor Ahmad alkardy
* As-Sheikh Dr saleh bn Muqbil
A taqaice wannan itace magana ta gaskiya akan halaccin tsotsar al’aura ga ma’aurata.      

                                              27/1/2016
Allah ne mafi sani.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button