Uncategorized

HADISIN KIRAN SALLAH A KUNNEN YARO BAYAN AN HAIFE SHI BAI INGANTA BA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HADISIN KIRAN SALLAH A KUNNEN YARO BAYAN AN HAIFE SHI BAI INGANTA BA


Jiya na yi rubutu akan hukuncin kiran sallah ga yaran da aka haifa, saidai wasu sun yi magangaanu akai. Na gode sosai da bayanan wasu daga cikin ‘yan’uwa, 
saidai kamar yadda wasu daga cikinku suka fada addini ba’a yinsa sai da hujja, don haka wadannan hadisai ba su inganta ba, 
shi ya sa ba za’a iya amfani da su ba, wasu daga cikin malamai sun yi amfani da kyautata hadisin da Albani ya yi, da kuma Tirmizi da ya inganta shi, wannan ne ya sa suke amfani da hadisin,
saidai shi Albani ya dawo daga rakiyar hadisin, ga abin da yake cewa : “Na taba kyautata hadisin kiran sallah a kunnen yaro ta hanyar SHAWAHID,
saboda ya zo da sanadi mai rauni a wajan Tirmizy,
sannan Baihaky ya rawaito shi da wani sanadin mai rauni a Shu’abul iman, to amma lokacin da na koma sanadin Shu’abul iman, sai na ga akwai maruwaita guda biyu wadanda ake zarginsu da karya, wannan ya sa na dawo daga rakiyar kyautata hadisin”,
saboda a wajan malamai, hadisin da yake akwai MATRUK, wato wanda ake zargi da karya, ba zai karfafi dan’uwansa ba.
Allah ne ma fi sani. 
    *Amsawa*
Dr.jamilu zarewa
posting by Abubakar Rabiu Yari
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button