Uncategorized

Shari’ar Da Sheik Abubakar Muhamud Gumi Yayi Wacce Ta Fi Ba Shi Mamaki

Shari’ar Da Sheik Abubakar Muhamud Gumi Yayi Wacce Ta Fi Ba Shi Mamaki
A rayuwar Malam an taba tambayar shi wacce shari’a ce wacce ya yi ta fi ba shi mamaki ko ba zai taba mantawa da ita ba.
Sai Malam ya ce, “akwai wata shari’a da na taba yi da tafi bani mamaki wanda ba zan manta da ita ba, a wani gari an yi wani attajiri da ya ke kasuwanci tare da wani mutum amma ba wanda ya san kudin ko na waye a cikinsu.
“Mutane na tsammani ko kudin nasu ne su biyu suka hada hannun jari suke kasuwanci. Ana nan haka, sai wata rana ciwon ajali ya kama wannan attaji, da ya ga ba halin tashi sai ya tara iyalansa da ‘yan uwansa da wasu mutane na daban ya ce, idan ya mutu dukiyar da ke hannun Alhaji wane tawa shi ce kadai bai da ko sisi ciki.
“Bayan nan wannan Attajiri sai ya rasu. Sai aka je wa da wannan dan’uwan kasuwancin nasa da wasiyar wannan Attajiri, aka ce Alhaji ya ce idan ya mutu asa dukiyar da ke hannunka a gado domin tashi ce shi kadai. Ko da ya ji haka sai ya tunbatse ya ce, Alhaji karya ya ke, wannan dukiya tashi ce shi kadai bai da ko kobo ciki. Ya ce kawai dai ya ja shi a jiki ne suna kasuwanci tare don ya samu wani abu.
Abu kamar wasa rigima har kotu. Akai ta rafka shari’a har Alhaji mai rai ya ce aje makabarta a tambayi Alhaji mai mutuwa dukiyar waye zai fadi ko ta waye. ‘Yan’uwan Alhaji mai mutuwa suka yarda duk da sun san ba’a mutuwa a dawo ballantana na kabari ya yi magana. Nan take aka rankaya da Alkali da lauyoyi da Alhaji mai rai da ‘yan’uwan Alhaji mai mutuwa aka nufi makabarta. Da aka je Alkali ya kira sunan Alhaji mai mutuwa. Bisa mamaki sai aka ji muryarsa ya amsa Alkali ya ce, “dukiyar daka mutu ka bari ta waye? Alhaji mai mutuwa ya ce, ta Alhaji wane ne ba tawa ba ce.”
Wannan abu ya tsorata Alkali har ya rasa yadda zai yi. Ga dai mamaci ya yi magana, abinda bai ko taba ji a wannan zamani ba.
Daga nan ne suka zo Kaduna wajen Alkali Sheikh Abubakar Muhamud Gumi a garin Kaduna. A lokacinsa ba Alkali irinsa. Nan take aka zo aka fada masa duk yadda abin ya faru tun daga mutuwar Alhaji har maganar da ya yi a kabari. Malam na ji ance mamaci yayi magana sai ya ce, “karya ne wanda ya mutu ba ya magana”, ya ce amma mu je inji da kunnena. Ya bisu har can garin aka je makabartan da Alhaji ke kwance aka nunawa Malam kabarin Alhaji, Malam ya kira sunan Alhaji, ya tambayi mamacin “dukiyar da ka mutu ka bari ta waye?” Alhaji ya ce “ba tawa bace, ta Alhaji wane ne (ya fadi sunan Alhaji mai rai). Wannan abu ya daurewa Malam kai, a ce mutum ya mutu yana kabari kwance kuma ya yi magana? Abin da mamaki”. Malam ya ce, “kowa ya tafi gida a dawo gobe.”
Daren ranar Malam bai rumtsa ba ya kawana nafila da addu’o’i akan wannan lamari.
Washegari aka dawo Makabarta tare da Alhaji mai rai da ‘yan uwan Alhaji mai mutuwa da lauyoyi da ‘yan sandan kotu, Malam ya ce wa ‘yan’uwan Alhaji, “zan sa a tone kabarin Alhaji kun yarda?” Suka ce, “sun yarda”. Malam ya sa aka kira masu gadin Makabarta ya umurcesu da su tone kabarin. Nan da nan suka kama aiki. Abin mamaki ana bude kabarin Alhaji sai aka ga layu da guraye da da su karhu da su baru kafi uwa-uba. Malam ya sa aka kwashe. Bayan an kwashe ya sa aka maida gawar Alhaji.
Bayan an rufeta Malam ya matsa kusa da kabarin Alhaji ya kira saunansa har sau uku Alhaji bai amsa ba. Malam ya ce, kudin da ka mutu ka bari na waye? Alhaji shiru ba amsa. Malam ya maimaita tambayar har sau uku shiru ba amsa. Sai ya waiwayo ya nuna Alhaji mai rai ya ce, “ku kama shi matsafi ne dukiyar marayu ya ke so ya cinye.”
To wannan shari’a ce tafi ba Malam mamaki da al’ajabi a rayuwar alkalancinsa. Fatanmu Allah Ya kiyaye mu da cin hakkin marayu kuma Ya jikan Malam da rahama ya sa ya huta, kuma Allah Ya jikan sauran al’ummar Musulmi bakidaya.
Madogara:Gumi Initiative Foundation
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button