Sports

NIGERIA TAYI NASARA KAN KASAR ZAMBIA DA 2-1(HOTUNA)

Nijeriya Ta Yi Nasara Kan Kasar Zambia Da Ci 2-1
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
A cigaba da wasannin neman gurbin shiga gasar kwallon kafa ta duniya da za a bugs s kasar Rasha a shekarar 2018, kungiyar kwallon kafan Nijeriya na Super Eagle yau ta yi nasara akan kungiyar kwallon kafan Zambia wanda ake mata lababi da Chipolopolo da ci biyu da daya.
Super Eagle ta samu wannan nasara ne ta kafar ‘yan wasan Nijeriya Alex Iwobi da Kelechi Iheanacho, suka zura kwallayen.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne ‘yan Zambia sukacyi ta maza inda a cikin mintona na 71 dan wasan Zambia mai suna Collins Mbesuma, ya zura kwallon daya a ragar Nijeriya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button