Uncategorized

LATESTNEWS:Hukumar EFCC ta kama wani tsohon Gwamna da dan sa

Hukumar EFCC ta karo tado maganar Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako
– Hukumar EFCC ta kama Tsohon Gwamnan da kuma dan sa, Abdul Azeez Nyako
– Abdul Azeez Nyako dai Sanata ne yanzu haka a Majalisar Dattawa
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kara kakkabe takardun Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa watau Murtala Nyako, da kuma ‘Dan sa; Abdul Azeez Nyako da kuma wasu mutanen na dabam. Hukumar EFCC ta dai maka su kara ne Babban Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja.
Hukumar EFCC ta kara shigar da karar Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Nyako a Kotun Kasar gaban Alkali Okon Abang. A bara dai Hukumar EFCC ta shiga da Tsohon Gwamnan Kotu gaban Marigayi Alkali Evoh Chukwu. A nan ne Alkali Chukwu ya bada belin tsohon Gwamnan da kuma dan sa na Miliyan 350
Ana dai zargin Tsohon Gwamnan na Jihar Adamawa, Murtala Nyako da sauran da laifi kusan guda 37; wadanda suka hada da satar kudin Gwamnatin Jihar Adamawa har biliyan 29. Rotimi Jacobs ne dai Lauyan da ke karar su Murtala Nyako, yayin da Kanu Agabi yake kare wadanda ake zargi, Nyako da dan sa dsr.
Ana zargin anyi amfani da wasu Kamfani wajen aikata wannan laifin irin su Blue Opal, Sabore Farms, Pagoda Fortunes, Tower Assets… Yanzu dai Alkali Abanga ya daga shari’ar da wata guda har zuwa Tsakiyar Nuwamba. Yace kuma za su cigaba da zama cikin belin da aka basu a baya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button